Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Ƴan sandan Pakistan sun daƙile harin ƙunar baƙin wake da aka kai wa wasu ƴan Japan

Hukumomi a Pakistan sun daƙile wani mumunan hari da aka yi ƙoƙarin kai wa wasu ƴan ƙasar Japan a yayin da suke dab da tsallake harin kwanton ɓauna da wasu ƴan bindiga suka shirya musu. Ƴan sanda a birnin Karachi da ke yankin kudancin Pakistan sun harbe wani ɗan ƙunar baƙin wake da kuma wasu ƴan b...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:08
Ƴan sandan Pakistan sun daƙile harin ƙunar baƙin wake da aka kai wa wasu ƴan Japan
A taƙaice

Hukumomi a Pakistan sun daƙile wani mumunan hari da aka yi ƙoƙarin kai wa wasu ƴan ƙasar Japan a yayin da suke dab da tsallake harin kwanton ɓauna da wasu ƴan bindiga suka shirya musu. Ƴan sanda a birnin Karachi da ke yankin kudancin Pakistan sun harbe wani ɗan ƙunar baƙin wake da kuma wasu ƴan b...

Hukumomi a Pakistan sun daƙile wani mumunan hari da aka yi ƙoƙarin kai wa wasu ƴan ƙasar Japan a yayin da suke dab da tsallake harin kwanton ɓauna da wasu ƴan bindiga suka shirya musu. Ƴan sanda a birnin Karachi da ke yankin kudancin Pakistan sun harbe wani ɗan ƙunar baƙin wake da kuma wasu ƴan bindiga a lokacin da suke ƙoƙarin kai hari kan wata mota mai ɗauke da wasu ƴan kasar Japan biyar, waɗanda dukkansu suka tsira, a cewar mai magana da yawun ƴan sandan. Ƴan bindigan waɗanda ke neman hamɓarar da gwamnati tare da kafa tsarin mulkinsu mai tsauri, sun ƙaddamar da wasu hare-hare mafi muni a Pakistan cikin ƴan shekarun da suka gabata, inda a wasu lokutan sukan kai hari kan ƴan kasashen waje, kamar ƴan China. Waɗanda suka tsira daga harin ƴan Japan ne kuma a halin da ake ciki suna ƙarƙashin kulawar jami'an, a cewar mai magana da yawun ƴan sandan, Abrar Hussain Baloch, a ranar Juma’a. Kawo yanzu dai babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin.