Главная / Архив новостей
Архив новостей

В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.

Ƴan sandan Isra'ila sun kama masu zanga-zangar neman a kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza

Jami'an tsaro sun kama masu zanga-zanga da dama saboda yin tarzoma, a cewar kafafen watsa labaran na ƙasar. Ƴan sandan Isra'ila sun kama mutum bakwai daga cikin masu zanga-zanga saboda yin tarzoma a kusa da Titin Begin don neman a kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza. “Jam'ain ƴan sa...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Обновлено 13.08.2026, 05:26:08
Ƴan sandan Isra'ila sun kama masu zanga-zangar neman a kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza
Кратко

Jami'an tsaro sun kama masu zanga-zanga da dama saboda yin tarzoma, a cewar kafafen watsa labaran na ƙasar. Ƴan sandan Isra'ila sun kama mutum bakwai daga cikin masu zanga-zanga saboda yin tarzoma a kusa da Titin Begin don neman a kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza. “Jam'ain ƴan sa...

Jami'an tsaro sun kama masu zanga-zanga da dama saboda yin tarzoma, a cewar kafafen watsa labaran na ƙasar. Ƴan sandan Isra'ila sun kama mutum bakwai daga cikin masu zanga-zanga saboda yin tarzoma a kusa da Titin Begin don neman a kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza. “Jam'ain ƴan sandan Isra'ila sun kama mutum 7 a Dandalin Kaplan da ke birnin Tel Aviv bisa zarginsu da yin tarzoma a yayin zanga-zangar da ke neman gwamnati ta sasanta da ƙungiar Hamas domin ta saki mutanen da ta yi garkuwa da su a Gaza," in ji jaridar Yedioth Ahronoth. Ta ƙara da cewa wasu masu zanga-zanga sun toshe hanyar da ake kira Begin Street -- wata hanya mai matuƙar muhimmanci a Tel Aviv -- a wani ɓangare na ƙoƙarin matsa lamba kan gwamnati don ta ɗauki mataki.​​​​​ A Yammacin Birnin Ƙudus, ɗaruruwan ƴan Isra'ila sun yi zanga-zanga a kusa da gidan Firaiminista Benjamin Netanyahu, inda suka buƙaci ya yi sulhu da ƙungiyar Falasɗinawa ta Hamas. Kazalika masu zanga-zangar sun yi kira a gudanar da zaɓe ba tare da ɓata lokaci ba, a cewar Yedioth Ahronoth. A yankin Caesarea da ke arewacin Isra'ila, mutum kimanin 1,200 sun yi zanga-zanga a kusa da gidan Netanyahu, inda suka buƙaci a saki mutanen da aka yi garkuwa da su sannan ya sauka daga mulki, kamar yadda kafar watsa labaran gwamnatin Isra'ila ta rawaito. Masu zanga-zangar sun riƙa yin ihu suna sukar gwamnatin Netanyahu inda suka dinga maimaita cewa, “A gudanar da zaɓe nan-take!” Haka kuma dubban Isra'ilawa sun yi zanga-zanga a wasu yankuna na ƙasar, ciki har da Haifa, Raanana da Rehovot.