الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

An samu sassaucin hauhawar farashin kayayyaki a Afrilu a Nijeriya – NBS

A sabuwar ƙididdigar da NBS ɗin ta fitar a ranar Alhamis, ta ce an samu raguwa daga kaso 24.23 da yake a Maris zuwa 23.71 a watan Afrilu. Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta fitar da sabbin bayanan ƙididdiga inda ta bayyana cewa an samu raguwar tashin farashin kayayyaki a ƙasar. A sabuwar ƙididd...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:08 ص
An samu sassaucin hauhawar farashin kayayyaki a Afrilu a Nijeriya – NBS
لمحة سريعة

A sabuwar ƙididdigar da NBS ɗin ta fitar a ranar Alhamis, ta ce an samu raguwa daga kaso 24.23 da yake a Maris zuwa 23.71 a watan Afrilu. Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta fitar da sabbin bayanan ƙididdiga inda ta bayyana cewa an samu raguwar tashin farashin kayayyaki a ƙasar. A sabuwar ƙididd...

A sabuwar ƙididdigar da NBS ɗin ta fitar a ranar Alhamis, ta ce an samu raguwa daga kaso 24.23 da yake a Maris zuwa 23.71 a watan Afrilu. Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta fitar da sabbin bayanan ƙididdiga inda ta bayyana cewa an samu raguwar tashin farashin kayayyaki a ƙasar. A sabuwar ƙididdigar da NBS ɗin ta fitar a ranar Alhamis, ta ce an samu raguwa daga kaso 24.23 da yake a Maris zuwa 23.71 a watan Afrilun 2025. A bara ne dai aka samu hauhawar farashin da aka shafe gomman shekaru ba a samu irinsa ba a ƙasar biyo bayan matakin da shugaban ƙasar ya ɗauka na karya darajar naira da kuma cire tallafin man fetur a lokacin da ya hau mulki a 2023. Haka kuma a binciken da NBS ɗin ta yi a matakin shekara, an samu raguwa a hauhawar farashi daga kaso 38.80 cikin 100 a watan Disamba zuwa 24.48 a watan Janairu. An ƙara samun raguwa a watan Fabrairu kafin ya ƙaru a Maris. Wani rahoto da NBS ɗin ta fitar ya nuna cewa a kayayyakin abinci da kuma barasa ne aka fi samun hawa da saukar farashi. A watan Maris, hauhawar farashin kayan abinci na kan 21.79 inda a watan Afrilu ya sauka zuwa 21.26.