Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

An saki Oscar Pistorius na Afirka ta Kudu daga gidan yari

An saki Pistorius a ranar Juma'a ne bayan ya shafe kusan shekaru 11 a gidan yari sakamakon samunsa da laifin harbe budurwarsa Reeva Steenkamp. An saki tsohon shahararren dan wasan tseren nakasassu na Afirka ta Kudu Oscar Pistorius daga gidan yari a ranarJuma’a, bayan ya shafe kusan shekaru 11 a t...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:08
An saki Oscar Pistorius na Afirka ta Kudu daga gidan yari
Em resumo

An saki Pistorius a ranar Juma'a ne bayan ya shafe kusan shekaru 11 a gidan yari sakamakon samunsa da laifin harbe budurwarsa Reeva Steenkamp. An saki tsohon shahararren dan wasan tseren nakasassu na Afirka ta Kudu Oscar Pistorius daga gidan yari a ranarJuma’a, bayan ya shafe kusan shekaru 11 a t...

An saki Pistorius a ranar Juma'a ne bayan ya shafe kusan shekaru 11 a gidan yari sakamakon samunsa da laifin harbe budurwarsa Reeva Steenkamp. An saki tsohon shahararren dan wasan tseren nakasassu na Afirka ta Kudu Oscar Pistorius daga gidan yari a ranarJuma’a, bayan ya shafe kusan shekaru 11 a tsare bisa laifin harbe budurwarsa Reeva Steenkamp, labarin da ya mamaye duniya. Sashen hukumar gyaran hali na Afirka ta Kudu ya tabbatar da sakinsa da safiyar ranar Juma'a yana mai cewa a halin yanzu "yana gida." Bayan ya shafe fiye da rabin hukuncin da aka yanke masa, dan wasan mai shekaru 37 da ya rasa kafafunsa biyu, ya bar gidan yarin Atteridgeville da ke wajen babban birnin kasar Pretoria. Pistorius ya shahara kuma an fi saninsa da "Blade Runner" a duniya saboda yadda aka kera kafafun karfen da ya ke amfani da su. Daga cikin sharadin sakinsa ba shi da 'yancin yi magana da kafafen yada labarai. Neman Afuwa da dama Hukumomin gidan yarin sun gargadi manema labarai cewa ba za a basu wata dama ta daukar shi hoto ba. Pistorius ya kashe budurwarsa Steenkamp, sarauniyar kyau mai shekara 29 a lokacin, da safiyar ranar masoya ta Valentine a shekarar 2013, inda ya yi harbi har sau hudu ta kofar bandakin gidansa da ke Pretoria. Harbin ya biyo bayan shekara guda da Pistorius ya kafa tarihi inda ya zama dan wasa na farko da ya lashe gasar Olympics a lokacin da ya fafata da wasannin da aka yi a London a shekarar 2012. An same shi da laifin kisan-kai kuma an yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekaru 13 a shekarar 2017 bayan dogon lokaci da aka kwashe ana shari’a da daukaka kara. Ya musanta aikata laifin da kuma musanta kashe Steenkamp, yana mai cewa ya yi zaton wani mahari ne ya yi kokarin shigo masa gida. Mahaifiyar Steenkamp ta ce ba ta yarda cewa ya fadi gaskiya kan abin da ya faru ba. Duba lafiyar Pistorius "'Yata ta yi kururuwar neman ceton rayuwarta, iya karfinta don makwabta su ji ta. Ban san abin da ya sanya shi harbi kusa da kofa ba," a cewar June Steenkamp a yayin da jawabinta a gaban kwamitin sassaucin kotu . Masu laifin a Afirka ta Kudu suna da 'yancin samun sassaucin hukunci kai-tsaye bayan sun cika rabin wa'adin da aka yanke musu. Da farko Pistorius ya yi rashin nasara wajen samun sassaucin hukuncin kotun a watan Maris lokacin da kwamitin ya gano bai kai rabin wa’adin da ake bukata na neman afuwa ba. A watan Oktoba Kotun tsarin mulkin kasar ta zartar da hukunci cewa ya aikata kuskure ne, matakin da ya share fagen sauraron karar da aka shigar a watan Nuwamba inda aka amince da sakinsa. Daga cikin sharuddan sakinsa, an bukaci daga yanzu har zuwa karshen wa'adin hukuncin da aka yanke masa a shekarar 2029, dole Pistorius ya duba lafiyarsa tare da neman shawarwari kan fushi da duk wani abu da ya shafi cin zarafin jinsi. An kuma hana shi shan barasa da sauran abubuwan saka maye da kuma zama a gida na wasu sa'o'i da aka ware a kowane rana. Duk da cewa June Steenkamp ba ta yi adawa da hukuncin sakin Pistorius ba kuma ta "gamsu" da sharuddan da aka gindaya masa, sai dai ba ta gamsu da cewa halinsa ya gyaru ba, a cewar mai magana da yawun danginta . "Babu wanda zai iya yin da-na-sani idan har bai amince da fadin gaskiya ba," in ji ta a cikin wata sanarwa.