Главная / Архив новостей
Архив новостей

В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.

An sake zabar Turkiyya mamba a Kungiyar Kasashe Masu Safara da Jiragen Ruwa

Ministan Sufuri da Ababen More Rayuwa na Turkiyya Abdulkadir Uraloglu ya bayyana cewa an zabi Turkiyya a matsayin mamba a kungiyar IMO “a karo na 13 a jere inda ta samu kuri’u mafi yawa a tarihi da goyon bayan kasashe 143." Ma’aikatar Harkokin Waje ta Turkiyya ta sanar da cewa an sake zabar Turki...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Обновлено 13.08.2026, 05:26:08
An sake zabar Turkiyya mamba a Kungiyar Kasashe Masu Safara da Jiragen Ruwa
Кратко

Ministan Sufuri da Ababen More Rayuwa na Turkiyya Abdulkadir Uraloglu ya bayyana cewa an zabi Turkiyya a matsayin mamba a kungiyar IMO “a karo na 13 a jere inda ta samu kuri’u mafi yawa a tarihi da goyon bayan kasashe 143." Ma’aikatar Harkokin Waje ta Turkiyya ta sanar da cewa an sake zabar Turki...

Ministan Sufuri da Ababen More Rayuwa na Turkiyya Abdulkadir Uraloglu ya bayyana cewa an zabi Turkiyya a matsayin mamba a kungiyar IMO “a karo na 13 a jere inda ta samu kuri’u mafi yawa a tarihi da goyon bayan kasashe 143." Ma’aikatar Harkokin Waje ta Turkiyya ta sanar da cewa an sake zabar Turkiyya domin kasancewa mamba a Kungiyar Kasashe Masu Safara da Jiragen Ruwa (IMO). A wata sanarwa da ma’aikatar ta saki, ta bayyana cewa an gudanar da zaben na IMO a ranar Juma’a a lokacin taron kungiyar na 33 da ake yi a birnin Landan. Turkiyya ta kasance ‘yar kungiyar kuma aka sake zabarta domin ci gaba da kasancewa a matsayin mamba, kamar yadda ma’aikatar ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar. “Turkiyya wadda aka zabeta a matsayin mamba a zaben da ake gudanarwa na kungiyar tun daga 1999, za ta ci gaba da bayar da gudunmawa mai yawa a aikin IMO, musamman duba da kwarewar da take da ita da gogewa ta fannin sufurin ruwa,” kamar yadda sanarwar ta kara da cewa. A yayin da yake karin bayani game da yadda aka gudanar da zaben, Ministan Sufuri da Ababen More Rayuwa na Turkiyya Abdulkadir Uraloglu ya bayyana cewa an zabi Turkiyya a matsayin mamba a kungiyar IMO “a karo na 13 a jere inda ta samu kuri’u mafi yawa a tarihi da goyon bayan kasashe 143.” “Baya ga goyon bayan da muka samu a zaben akwai manufofi masu nasara da kuma matakai na hakika da muka dauka daidai da dokokin kasa da kasa a fannin teku, da kuma yadda muke aiki tukuri a ayyukan IMO.”