Tsawon kwanaki 108, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 25,295 da raunata mutum 63,000. 0230 GMT — An sake jikkata sojojin Isra’ila 19 a yakin Gaza – Rundunar soji Rundunar sojin Isra'ila a ranar Litinin ta ce an sake jikkata wasu sojojinta 19 a Zirin Gaza cikin awa 24 da suka wuce. Alkaluman da sojojin suka fitar sun nuna cewa sojoji 1,222 ne suka jikkata tun bayan da Isra'ila ta fadada kai hare-hare ta kasa a Zirin Gaza a ranar 27 ga watan Oktoba. Alkaluman sun ce sojoji 532 aka kashe yayin da wasu 2,672 suka jikkata tun bayan barkewar rikicin Gaza a watan Oktoba. 0140 GMT — Sojojin Isra'ila sun kai hari asibitin Al Khair na Gaza, tare da yiwa wani asibiti ƙawanya Jami'an Falasdinawa sun ce sojojin Isra'ila sun shiga cikin yammacin Khan Younis a yakin da aka yi mafi muni a Zirin Gaza tun kamawar sabuwar shekara, inda suka kutsa kai cikin wani asibiti tare da killace wani, da kuma cire masu samun kulawa ta musamman daga sashen gaggawa. A karon farko sojoji sun kutsa cikin gundumar al Mawasi da ke kusa da gabar tekun Bahar Rum da yammacin Khan Younis da babban birnin da ke kudancin Gaza a ranar Litinin. A can ne suka kutsa kai asibitin Al Khair kuma suka kame ma'aikatan lafiya kamar yadda kakakin ma'aikatar lafiya ta Gaza Ashraf al Qidra ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters. Kawo yanzu dai babu wani bayani daga Isra'ila kan halin da ake ciki a asibitin. Ofishin kakakin rundunar sojin bai ce komai ba. 1140 GMT — Isra'ila ta kai hari kan makarantun da Falasdinawa 30,000 da suka rasa matsugunansu ke samun mafaka Harin ya yi sanadin rayukan mutane da dama tare da jikkata wasu da suka nemi mafaka / Photo: Reuters Sojojin Isra'ila sun kai hari kan jami'o'i biyu da makarantu uku da Falasdinawa 30,000 da suka rasa matsugunansu a garin Khan Younis da ke kudancin Gaza ke samun mafaka a wajen, inda suka kai hare-hare ta sama da kuma ruwan wuta, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama. Sanarwar da ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya fitar ta ce sojojin sun kai harin wasu matsugunai guda biyar a Khan Younis da ke dauke da mutum 30,000 da suka rasa matsugunansu. Sanarwar ta ce sojojin na Isra'ila sun yi amfani da jiragen leƙen asiri da harsasai wajen kai hari a Jami'ar Al Aqsa, da Kwalejin Koyon Kimiyya ta Jami'ar, da makarantar Khaledia, da makarantar Al Mawasi, da makarantar masana'antu a Khan Younis. Harin ya yi sanadin rayukan mutane da dama tare da jikkata wasu da suka nemi mafaka a matsugunan da Isra'ila ta yi ikirarin cewa suna cikin aminci. 1255 GMT — EU tana neman a samar da kasar Falasdinu mai cin gashin kanta Ministocin Ƙungiyar Tarayyar Turai sun yi muhawara kan ko ƙirƙirar ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta ce kawai mafita wajen samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya, tare da bayyana damuwarsu a kan yadda Firaiminista Benjamin Netanyahu yake watsi da batun. "Matsayar Benjamin Netanyahu abin damuwa ce. Akwai buƙatar samar da ƙasar Falasɗinu mai tabbacin tsaro ga kowa," kamar yadda Ministar Harkokin Wajen Faransa Stephane Sejourne ta shaida wa manema labarai a Brussels, inda ministocin EU suka gana don tattauna batun yaƙin Gaza. Ministan Harkokin Wajen Isra'ila Katz da takwaransa na Jordan Ayman Safadi ma sun halarci tattaunawar da aka yi a babban birnin ƙasar Belgium. Batun makomar Gaza ya kuma sa an samu rashin jituwa tsakanin Isra'ila da Amurka da ƙawayenta na yankin Larabawa, a yayin da suke ƙoƙrin shiga tsakani don kawo ƙrshen yaƙin da ake yi a yankin Falasɗinu. 1210 GMT — Isra'ila ta kashe karin Falasdinawa 190 a kwana guda a Gaza Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan kaso 85 cikin 100 na Falasdinawa sun rasa muhallansu sakamakon hare-haren Isra'ila. / Hoto: AP Akalla Falasdinawa190 Isra’ila ta kashe a Gaza da raunata wasu 340 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata. Hakan ya kawo adadin Falasdinawan da Isra’ilar ta kashe a Gaza zuwa 25,295 kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta tabbatar. A wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta bayyana akwai mutum 63,000 wadanda aka raunata tun bayan da aka soma kai wannan harin
Архив новостей
В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.
An sake jikkata sojojin Isra’ila 19 a yakin Gaza – Rundunar soji
Tsawon kwanaki 108, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 25,295 da raunata mutum 63,000. 0230 GMT — An sake jikkata sojojin Isra’ila 19 a yakin Gaza – Rundunar soji R...

Кратко
Tsawon kwanaki 108, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 25,295 da raunata mutum 63,000. 0230 GMT — An sake jikkata sojojin Isra’ila 19 a yakin Gaza – Rundunar soji R...
