Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

An kashe 'yan Sudan sha shida a Sudan ta Kudu: 'yan sanda

Rundunar 'yan sandan Sudan ta Kudu ta sanar a ranar Litinin cewa an kashe 'yan Sudan 16 a wata tarzoma a makon jiya kan zargin kashe-kashen 'yan Sudan ta Kudu a yankin Al Jazirah na Sudan. Rundunar ‘yan sandan Sudan ta Kudu ta sanar a ranar Litinin cewa an kashe ‘yan kasar Sudan 16 a tarzomar da...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:08
An kashe 'yan Sudan sha shida a Sudan ta Kudu: 'yan sanda
De un vistazo

Rundunar 'yan sandan Sudan ta Kudu ta sanar a ranar Litinin cewa an kashe 'yan Sudan 16 a wata tarzoma a makon jiya kan zargin kashe-kashen 'yan Sudan ta Kudu a yankin Al Jazirah na Sudan. Rundunar ‘yan sandan Sudan ta Kudu ta sanar a ranar Litinin cewa an kashe ‘yan kasar Sudan 16 a tarzomar da...

Rundunar 'yan sandan Sudan ta Kudu ta sanar a ranar Litinin cewa an kashe 'yan Sudan 16 a wata tarzoma a makon jiya kan zargin kashe-kashen 'yan Sudan ta Kudu a yankin Al Jazirah na Sudan. Rundunar ‘yan sandan Sudan ta Kudu ta sanar a ranar Litinin cewa an kashe ‘yan kasar Sudan 16 a tarzomar da ta barke a makon da ya gabata saboda zargin kisan gillar da aka yi wa ‘yan Sudan ta Kudu a yankin Al Jazirah na kasar Sudan. A ranakun Alhamis da Juma'a ne rikicin ya ɓarke a Juba babban birnin Sudan ta Kudu da kuma wasu wurare na ƙasar, inda masu zanga-zangar suka fusata kan abin da suka yi imani cewa da hannun sojojin Sudan da ƙungiyoyin ƙawayenta wajen kashe-kashen Al Jazirah. Rundunar sojin Sudan ta yi Allah-wadai da abin da ta kira ‘’cin zarafi na ɗaiɗaikun mutane’’ a birnin Al Jazira bayan ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama sun ɗora alhakin hare-haren na ƙabilanci a kan fararen hula da ake zargi da tallafa wa 'yan tawayen rundunar RSF. A cikin wata sanarwa da rundunar 'yan sandan Sudan ta Kudu ta fitar, ta ce ‘’an kashe 'yan Sudan 16 a jihohi hudu.’’ Dokar hana fitar dare ‘Yan sanda za su ci gaba da sintiri a kasuwanni da wuraren zaman jama’a domin al’ummar Sudan, a cewar sanarwar. A ranar Juma'a ne, gwamnati ta kafa dokar hana fitar dare zuwa safiya, wacce har yanzu take aiki. Aƙalla mutane 24 ne aka kama kuma za a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala bincike, in ji rundunar sojin Sudan ta Kudu a wata sanarwa ta daban da ta fitar.