Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

An kashe mutane da dama a Mozambique kan sakamakon zaɓe

Mutane da dama ne aka bayar da rahoton sun rasa rayukansu sakamakon zanga-zangar zaɓen shugaban ƙasa a Mozambique, zaɓen da ɗan takarar Jam’iyyar FRELIMO wato Daniel Chapo ya yi nasara. Aƙalla mutum 10 ne aka kashe sakamakon zanga-zangar zaɓen shugaban ƙasa na 9 ga watan Oktoba a Mozambique, zaɓe...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:08
An kashe mutane da dama a Mozambique kan sakamakon zaɓe
Kwa muhtasari

Mutane da dama ne aka bayar da rahoton sun rasa rayukansu sakamakon zanga-zangar zaɓen shugaban ƙasa a Mozambique, zaɓen da ɗan takarar Jam’iyyar FRELIMO wato Daniel Chapo ya yi nasara. Aƙalla mutum 10 ne aka kashe sakamakon zanga-zangar zaɓen shugaban ƙasa na 9 ga watan Oktoba a Mozambique, zaɓe...

Mutane da dama ne aka bayar da rahoton sun rasa rayukansu sakamakon zanga-zangar zaɓen shugaban ƙasa a Mozambique, zaɓen da ɗan takarar Jam’iyyar FRELIMO wato Daniel Chapo ya yi nasara. Aƙalla mutum 10 ne aka kashe sakamakon zanga-zangar zaɓen shugaban ƙasa na 9 ga watan Oktoba a Mozambique, zaɓen da ɗan takarar Jam’iyyar FRELIMO wato Daniel Chapo ya yi nasara. Wata kungiya mai zaman kanta ta CIP ta kasar, ta ce an samu labarin mace-mace a sassa daban-daban na kasar biyo bayan tashe-tashen hankula da suka biyo bayan zaben kasar, sakamakon zanga-zangar da matasa suka yi. Maputo babban birnin kasar Mozambique ya sha da kyar a ranar Alhamis a zanga-zangar bayan da aka ayyana Chapo a matsayin wanda ya lashe kusan kashi 71% na kuri'un da aka kaɗa. Jam'iyyar FRELIMO ce ke mulki a Mozambique tun bayan samun 'yancin ƙasar daga Portugal a 1975. An ƙona ofishin Jam'iyyar FRELIMO Ɗan takara mai zaman kansa Venancio Mondlane, mai goyon bayan masu fatan ci gaban Mozambique (PODEMOS), shi ya zo na biyu da kashi 20% na kuri'un da aka kada. Dan takarar babbar jam'iyyar adawa Ossufo Momade na jam'iyyar RENAMO ya zo na uku da kusan kashi 6% na kuri'un da aka kada. Kafofin yada labaran Mozambique sun ruwaito cewa masu zanga-zangar sun kona ofisoshin jam'iyyar FRELIMO mai mulki uku, yayin da aka fasa shaguna da dama aka sace kayayyaki tare da kona motoci. An kama daruruwan mutane, inda alƙaluman 'yan sanda ke nuna cewa akwai mutum 20 waɗanda suka jikkata yayin wannan zanga-zanga. Shugaban ƙasa ya buƙaci a zauna lafiya 'Yan sanda sun kuma ce akalla jami'ai takwas ne suka jikkata a zanga-zangar, kuma an fara shari'ar masu laifi 44 da ake zargi. An tilasta wa 'yan sanda jefa hayaƙi mai sa hawaye domin tarwatsa zanga-zangar, wadda ta samo asali daga zargin magudin zabe da aka yi domin goyon bayan jam'iyya mai mulki. Tuni dai kungiyar ta RENAMO ta yi kira da a soke sakamakon zaben. Jami'an tsaro a Mozambique har yanzu ba su bayar da alkaluman adadin wadanda suka mutu a hukumance ba, sai dai kafafen yada labarai da dama a Mozambique sun bayar da rahoton cewa an samu asarar rayuka a zanga-zangar da ake ci gaba da yi. Shugaban Mozambique mai barin gado Filipe Nyusi, wanda ya gama kammala wa'adinsa na biyu, ya bukaci 'yan kasar da su kwantar da hankalinsu kafin bayyana sakamakon zabe.