Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

An kashe mutane da dama a hare-haren da aka kai a arewa maso yammacin Pakistan cikin sa'o'i 24: Sojoji

Hare-haren na zuwa ne a lokacin da mayakan suke sake ci gaba da kai hare-hare a yankin arewa maso yammacin kasar da ke kan iyaka da kasar Afganistan, wanda a watan da ya gabata ne gwamnatin kasar ta kaddamar da farmakin yaki da ta'addanci a yankin. Akalla mutane 28 da suka haɗa da fararen hula bi...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:08
An kashe mutane da dama a hare-haren da aka kai a arewa maso yammacin Pakistan cikin sa'o'i 24: Sojoji
Kwa muhtasari

Hare-haren na zuwa ne a lokacin da mayakan suke sake ci gaba da kai hare-hare a yankin arewa maso yammacin kasar da ke kan iyaka da kasar Afganistan, wanda a watan da ya gabata ne gwamnatin kasar ta kaddamar da farmakin yaki da ta'addanci a yankin. Akalla mutane 28 da suka haɗa da fararen hula bi...

Hare-haren na zuwa ne a lokacin da mayakan suke sake ci gaba da kai hare-hare a yankin arewa maso yammacin kasar da ke kan iyaka da kasar Afganistan, wanda a watan da ya gabata ne gwamnatin kasar ta kaddamar da farmakin yaki da ta'addanci a yankin. Akalla mutane 28 da suka haɗa da fararen hula biyar da sojoji 10 da kuma wasu da ake zargin 'yan bindiga 13 ne aka kashe a hare-haren da aka kai a arewa maso yammacin Pakistan cikin sa'o'i 24 da suka gabata, a cewar wata sanarwa da rundunar sojin kasar ta fitar. Wani harin da aka kai a wani sansanin soji da ke arewa maso yammacin Pakistan a ranar Litinin ya kashe jami’an tsaro takwas, kamar yadda rundunar sojin ta sanar a ranar Talata, bayan da wani ɗan ƙunar baƙin wake ya tayar da wata mota dauke da bama-bamai a jikin wata katanga. Jami'an tsaro sun kashe dukkan maharan guda 10 da ke da hannu a lamarin, kamar yadda wata sanarwa da rundunar ta fitar ta faɗa. Daga cikin wadanda suka mutu a harin na ranar Litinin har da sojoji bakwai da sojan sa-kai guda daya. Wani hari na biyu da aka kai ranar Talata a wata cibiyar kiwon lafiya a arewa maso yammacin Pakistan ya kashe mutane bakwai da suka hada da ma'aikatan kiwon lafiya da yara da sojoji, in ji rundunar sojin kasar a ranar Talata. An kashe dukkan mayaƙan sa kan uku a wani harin mayar da martanin da dakarun tsaro suka yi, in ji sanarwar. Wannan dai shi ne hari na biyu na ‘yan bindiga da aka sanar a cikin sa’o’i 24 a arewa maso yammacin Pakistan.