Rahoton da kamfanin tsaro na Beacon Consulting ya fitar a Nijeriya ya ce mutum 9,734 sun rasu sakamakon hare-haren ayyukan ta'addanci a fadin kasar, akasari a arewacin kasar. Kamfanin tsaro na Beacon Consulting a Nijeriya ya bayyana cewa mutum 9, 734 sun rasa rayukansu sakamakon ayyukan ta’addanci a fadin kasar a shekarar 2023. A wani rahoto na musamman da kamfanin ya fitar, ya yi kididdiga dangane da kiyasin ayyukan ta’addanci da aka yi a kasar tun daga farkon shekarar har zuwa karshenta. A watanni shidan farko na shekarar, kamfanin ya ce mutum 4,574 sun rasa rayukansu inda aka sace mutum 1,489 a hare-hare 2,512. Sannan a watanni shida na karshen shekarar mutum 5,160 ne suka rasu sannan aka sace 2,560 a hare-hare 4,003. Mace-mace Kamfanin na Beacon Consulting ya yi kididdigar mace-macen da aka samu dangane da yankunan Nijeriya. - A Arewa ta Tsakiyar Nijeriya mutum 1,114 ne suka rasu a watanni shidan farkon shekarar, sannan mutum 888 suka rasu bayan nan. - A Arewa Maso Gabashin Nijeriya mutum 1,375 ne suka mutu a watanni shidan farkon shekarar, sannan mutum 2,037 suka rasu bayan nan. - Sannan a Arewa Maso Yammacin Nijeriya mutum 1,126 suka rasu a watannin farkon shekarar sannan 1,164 a watannin karshen shekara. - A Kudu Maso Gabashin Nijeriya kuwa mutum 319 ne suka rasu a watanni shidan farko sannan 239 suka rasu a watannin shidan karshe. - A Kudu Maso Kudancin Nijeriya mutum 280 suka rasu a watannin shidan farkon shekarar sannan 418 suka rasu a watannin shidan karshe duk a sakamakon ta’addanci. Garkuwa da mutane Dangane da batun garkuwa da mutane a 2023, kamfanin na Beacon Consulting ya fitar da ƙididdiga dangane da wadanda aka sace a 2023. - A Arewa Maso Tsakiyar Nijeriya, mutum 1,006 aka yi garkuwa da su a yankin. - Sannan kuma a Arewa Maso Gabashin Nijeriya, mutum 795 aka sace a yankin. - Haka kuma a Arewa Maso Yammacin Nijeriya, mutum 1,728 aka sace a yankin. - Sai kuma a Kudu Maso Gabashin Nijeriya, mutum 165 aka sace a yankin. - A Kudu Maso Yammacin Nijeriya kuwa, mutum 169 ne aka sace a yankin. - Sai kuma a Kudu Maso Kudancin Nijeriya, mutum 186 aka sace a yankin.
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
An kashe kusan mutum 10,000 tare da yin garkuwa da sama da 4,000 a Nijeriya a 2023
Rahoton da kamfanin tsaro na Beacon Consulting ya fitar a Nijeriya ya ce mutum 9,734 sun rasu sakamakon hare-haren ayyukan ta'addanci a fadin kasar, akasari a arewacin kasar. Kamfanin tsaro na Beacon Consulting a Nijeriya ya bayyana cewa mutum 9, 734 sun rasa rayukansu sakamakon ayyukan ta’addanc...

Rahoton da kamfanin tsaro na Beacon Consulting ya fitar a Nijeriya ya ce mutum 9,734 sun rasu sakamakon hare-haren ayyukan ta'addanci a fadin kasar, akasari a arewacin kasar. Kamfanin tsaro na Beacon Consulting a Nijeriya ya bayyana cewa mutum 9, 734 sun rasa rayukansu sakamakon ayyukan ta’addanc...
