Wata sanarwa da Muƙaddashiyar Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta Rundunar Sojan Nijeriya Laftanal Kanal Appolonia Anele ta fitar a ranar Litinin ta ambaci sunan kwamandan a matsayin Laftanal Kanal Aliyu Paiko. Rundunar sojan Nijeriya ta ce wani kwamanda da wasu sojoji na rundunar Operation Hadin Kai sun rasa ransu a yayin wata arangama da mayaƙan Boko Haram a Jihar Borno a ranar Juma’a 17 ga watan Oktoba. Wata sanarwa da Muƙaddashiyar Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta Rundunar Sojan Nijeriya Laftanal Kanal Appolonia Anele ta fitar a ranar Litinin ta ambaci sunan kwamandan a matsayin Laftanal Kanal Aliyu Paiko. Sai dai ba ta ambaci yawan sojojin da aka kashe a arangamar ba, amma ta bayyana cewa kaɗan ne. A ɓangare ɗaya kuma ta ce an kashe ‘yan Boko Haram da dama, an kuma ji wa wasu masu yawa rauni. Appolonia Anele ta ce lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Bama ta jihar Borno, yayin da sojojin suka gano kuma suka lalata wani sansanin Boko Haram a lokacin da suke shirin kai wa jama’a hare-hare. “Waɗannan jajirtattun gwararzan sun rasa ransu, saboda ƙasarmu, don haka za a ci gaba da tunawa da su har abada. Rundunar Sojan Nijeriya za ta ci gaba da martaba sadaukarwarsu, saboda rashinsu ya zo tare da ƙudirinmu na kawar da ta’addanci daga Nijeriya,” a cewar sanarwar. Sanarwar ta kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su guji wallafa hotunan jami’an da suka rasa ransu yayin fafatawar, har zuwa lokacin da za a sanar da iyalensu a hukumance, domin tausayawa da kuma mutuntawa a gare su.
Haber arşivi
Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.
An kashe jami'ai a harin Boko Haram da sojoji suka daƙile a Jihar Borno
Wata sanarwa da Muƙaddashiyar Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta Rundunar Sojan Nijeriya Laftanal Kanal Appolonia Anele ta fitar a ranar Litinin ta ambaci sunan kwamandan a matsayin Laftanal Kanal Aliyu Paiko. Rundunar sojan Nijeriya ta ce wani kwamanda da wasu sojoji na rundunar Operati...
Bu haberde ne var?
Wata sanarwa da Muƙaddashiyar Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta Rundunar Sojan Nijeriya Laftanal Kanal Appolonia Anele ta fitar a ranar Litinin ta ambaci sunan kwamandan a matsayin Laftanal Kanal Aliyu Paiko. Rundunar sojan Nijeriya ta ce wani kwamanda da wasu sojoji na rundunar Operati...
