Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

An kashe babban ɗan adawa na gwamnatin Chadi yayin da ake cikin hargitsi a babban birnin

Dillo shi ne babban ɗan adawa da shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya wanda ya kasance ɗan'uwansa, wato Mahamat Idriss Deby Itno. An kashe shugaban ƴan adawa na Chadi Yaya Dillo a ranar Laraba yayin wata musayar wuta da jami'an tsaro, kamar yadda babban mai shigar da ƙara Oumar Mahamat Kedelaye ya faɗ...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:08
An kashe babban ɗan adawa na gwamnatin Chadi yayin da ake cikin hargitsi a babban birnin
En bref

Dillo shi ne babban ɗan adawa da shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya wanda ya kasance ɗan'uwansa, wato Mahamat Idriss Deby Itno. An kashe shugaban ƴan adawa na Chadi Yaya Dillo a ranar Laraba yayin wata musayar wuta da jami'an tsaro, kamar yadda babban mai shigar da ƙara Oumar Mahamat Kedelaye ya faɗ...

Dillo shi ne babban ɗan adawa da shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya wanda ya kasance ɗan'uwansa, wato Mahamat Idriss Deby Itno. An kashe shugaban ƴan adawa na Chadi Yaya Dillo a ranar Laraba yayin wata musayar wuta da jami'an tsaro, kamar yadda babban mai shigar da ƙara Oumar Mahamat Kedelaye ya faɗa. An ji ƙarar harbe-harbe a ranar Laraba a N'Djamena, babban birnin ƙasar a kusa da hedikwatar jam'iyyar adawa, a cewar wani ganau na Reuters, bayan da tun da fari aka kashe mutane da dama a wani hargitsin da ya faru a ofishin hukumar tsaron cikin gida ta ƙasar. Hukumomi sun zargi masu fafutuka na jam'iyyar adawa ta Socialist Party Without Borders (PSF), wacce Dillo ke jagoranta da tayar da hargitsin. Dillo shi ne babban ɗan adawa da shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya wanda ya kasance ɗan'uwansa, wato Mahamat Idriss Deby Itno. An saka ranar 6 ga watan Mayu a matsayin wacce za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa, inda Devy da Dillo duka suka ayyana aniyarsu ta tsayawa takara.