Mai daukar hoto na gidan talebijin din FOX 7, Austin na daga cikin mutanen da aka kama a yayin zanga-zangar goyon bayan Falasdinu a sansanonin Jami'ar Texas da ke Amurka. Adadin masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu da aka kama a yayin wata zanga-zanga a Jami'ar Texas ta Amurka ya kai 34, a cewar hukumomi. "Ya zuwa karfe 9 na dare, jami'an tsaro sun kama mutum 34 a harabar Jami'ar UT Austin biyo bayan zanga-zangar yau da aka gudanar," a cewar wani sako da Ma'aikatar Tsaron Al'umma ta Texas ta wallafa a shafinta na X, wanda a baya ake kira Twitter, a ranar Laraba. Daga cikin wadanda aka kama har da wani mai ɗaukar hoto na gidan talabijin din FOX 7, Austin wanda ke daukar hoton zanga-zangar daliban a harabar Jami'ar UT Austin. Hotunan soshiyal midiya sun nuna yadda aka kwantar da mai ɗaukar hoton a ƙasa kana aka ɗaure masa hannayensa. Daliban sun gudanar da wani tattaki ne domin neman jami'ar ta janye kanta daga ƙera makaman da ke da alaƙa da Isra'ila. Zanga-zangar ta rikiɗe zuwa tashin hankali bayan da dakarun Sashen Tsaron Al'umma na Texas suka kutsa kai cikin taron. This video is unbelievable. Students and teachers are being arrested for protesting US support for atrocities in Gaza. Now reporters are getting assaulted and arrested for covering the protests. But remember, democracy is on the ballot. pic.twitter.com/Gsl1zbnPKq — Assal Rad (@AssalRad) April 24, 2024 Tattakin wani bangare ne na zanga-zangar gama gari na nuna goyon baya ga Falasdinu inda aka buƙaci cibiyoyin ilimi su janye daga kamfanonin da ke kasuwanci da Isra'ila. Sai dai Ma'aikatar Tsaron al'umma DPS ta ce tana mayar da martani ne bisa ga bukatar jami'ar da kuma Gwamna Greg Abbott. Abbott ya ce za a ci gaba da kamen har sai taron ya watse.
Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.
An kama mutum 34 lokacin zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Amurka
Mai daukar hoto na gidan talebijin din FOX 7, Austin na daga cikin mutanen da aka kama a yayin zanga-zangar goyon bayan Falasdinu a sansanonin Jami'ar Texas da ke Amurka. Adadin masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu da aka kama a yayin wata zanga-zanga a Jami'ar Texas ta Amurka ya kai 34, a cew...

Mai daukar hoto na gidan talebijin din FOX 7, Austin na daga cikin mutanen da aka kama a yayin zanga-zangar goyon bayan Falasdinu a sansanonin Jami'ar Texas da ke Amurka. Adadin masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu da aka kama a yayin wata zanga-zanga a Jami'ar Texas ta Amurka ya kai 34, a cew...
