Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

An kama jirgin ruwa ɗauke da 'yan ci-rani sama da 200 da ke hanyar zuwa Turai

Sojojin Senegal ne suka kama jirgin ruwan, makonni bayan wani jirgin ruwan ya kashe kusan mutum 90 a hanyarsu ta zuwa Mauritania daga Senegal. Rundunar Sojin Senegal a ranar Asabar ta ce ta kama wani jirgin ruwa wanda ke ɗauke da ‘yan ci-rani sama da 200 waɗanda ke hanyarsu ta zuwa Turai. A wata...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:07
An kama jirgin ruwa ɗauke da 'yan ci-rani sama da 200 da ke hanyar zuwa Turai
At a glance

Sojojin Senegal ne suka kama jirgin ruwan, makonni bayan wani jirgin ruwan ya kashe kusan mutum 90 a hanyarsu ta zuwa Mauritania daga Senegal. Rundunar Sojin Senegal a ranar Asabar ta ce ta kama wani jirgin ruwa wanda ke ɗauke da ‘yan ci-rani sama da 200 waɗanda ke hanyarsu ta zuwa Turai. A wata...

Sojojin Senegal ne suka kama jirgin ruwan, makonni bayan wani jirgin ruwan ya kashe kusan mutum 90 a hanyarsu ta zuwa Mauritania daga Senegal. Rundunar Sojin Senegal a ranar Asabar ta ce ta kama wani jirgin ruwa wanda ke ɗauke da ‘yan ci-rani sama da 200 waɗanda ke hanyarsu ta zuwa Turai. A wata sanarwa da sojojin suka fitar a shafinsu na X, sun bayyana cewa wani jirgin ruwan soji wanda ke shawagi ne ya gano jirgin a ranar Juma’a ɗauke da mutum 202, daga ciki har da mata biyar da ƙaramin yaro. A farkon watan Yulin nan, wani jirgin ruwa ɗauke da kusan mutum 170 wanda ya bar Senegal zuwa Mauritania ya kashe kusan mutum 90 bayan ya kife. Wannan bala’in ne ya jawo Firaiministan Senegal Ousmane Sonko ya yi magana da babbar murya inda ya roƙi mutane da su daina kasada suna sayar da rayuwarsu ta hanyar shiga irin waɗannan jiragen ruwan masu cunkoso. Le patrouilleur Cayor a intercepté ce jour, au large de Lompoul, une pirogue transportant 202 candidats à l’émigration irrégulière dont cinq femmes et un mineur. Tous les migrants ont été débarqués à Dakar et remis aux services compétents. pic.twitter.com/NpVuosu1Ku — Marine nationale sénégalaise (@MarineNation_SN) July 19, 2024 Sai dai duk da haka masu tafiya ci-ranin zuwa Turai a halin yanzu suna ƙara bin wannan hanya duk da yadda ake ƙara tsaurara tsaro a cikin tekun. “Ina sake kira ga matasa: ba za ku magance matsalolinku a cikin jirgin ruwa ba,” kamar yadda Sonko ya shaida wa taron wasu matasa a Saint-Louis. “Makomar duniyar nan ita ce Afirka... wadda ita ce nahiyar da har yanzu take da akamun samun ci gaba.” Kamar yadda wata ƙungiya mai zaman kanta ta Sifaniya Caminando Fronteras ta bayyana, sama da mutum 5,000 suka rasua hanyarsu ta zuwa Sifaniya ta teku a watanni biyar na farkon wannan shekarar, wanda wannan shi ne adadi mafi yawa tun bayan da ƙungiyar ta soma aikin tattara alƙaluma a 2007.