Mutane sun mutu sannan wasu suka jikkata a yayin da wasu ƴan bindiga suka kai hare-hare a lokaci guda a sansanonin soji guda biyu da ofishin ƴan sanda a babban birnin Chabahar da kuma birnin Rask, a cewar jami'a. Aƙalla jami'an tsaro uku sun mutu a wasu hare-hare da aka kai a lokaci guda a sansanonin soji da lardin Sistan and Baluchestan da ke kudu maso gabashin Iran, a cewar kafofin watsa labarai da jami'an gwamnatin ƙasar. Kamfanin dillancin labarai na IRNA, wanda ya ambato wasu majiyoyi suna tabbatar da kai hare-haren, ya ce an kai "hare-haren ta'addanci guda uku" a lokaci guda a sanyin safiyar Alhamis a ofishin ƴan sanda da kuma sansanonin soji guda biyu a babban irnin Chabahar da kuma birnin Rask. IRNA ya ce an jikkata aƙalla mahara uku tare da kashe ɗaya a wani martani da ƴan sanda suka mayar. Ana ci gaba da farautar maharan, in ji IRNA. An kashe jami'an tsaro aƙalla uku yayin hare-haren, a cewar kafofin watsa labarai na ƙasar. Rahoton IRNA bai bayyana ɓarnar da aka yi wa ƴan sanda ba, sai dai rahotanni sun ce mai yiwuwa an tafka musu mummunar ɓarna. IRNA da wasu kafofin watsa labaran Iran sun ambato mataimakin gwamnan lardin yana cewa wani mahari ya yi yunƙurin shiga hedkwatar Rundunar Juyin-Juya-Hali ta Islamic Revolutionary Guard Corps ( IRGC) da ke Rask amma an hana shi.
Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.
An kai hari a sansanonin soji a lardin Sistan and Baluchestan na ƙasar Iran
Mutane sun mutu sannan wasu suka jikkata a yayin da wasu ƴan bindiga suka kai hare-hare a lokaci guda a sansanonin soji guda biyu da ofishin ƴan sanda a babban birnin Chabahar da kuma birnin Rask, a cewar jami'a. Aƙalla jami'an tsaro uku sun mutu a wasu hare-hare da aka kai a lokaci guda a sansan...

Mutane sun mutu sannan wasu suka jikkata a yayin da wasu ƴan bindiga suka kai hare-hare a lokaci guda a sansanonin soji guda biyu da ofishin ƴan sanda a babban birnin Chabahar da kuma birnin Rask, a cewar jami'a. Aƙalla jami'an tsaro uku sun mutu a wasu hare-hare da aka kai a lokaci guda a sansan...
