Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

An ji wa Shugabaan Comoros rauni a harin da aka kai masa da wuƙa

Shugaba Azali Assoumani ya koma gida bayan harin, kamar yadda mai magana da yawun gwamnati ta faɗa. Shugaban Comoros Azali Assoumani ya samu rauni kadan a wani harin wuka da aka kai masa a ranar Juma'a, kakakin gwamnatin kasar ta ce an tsare maharin. Lamarin ya faru ne da misalin karfe biyu na ra...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:07
An ji wa Shugabaan Comoros rauni a harin da aka kai masa da wuƙa
De un vistazo

Shugaba Azali Assoumani ya koma gida bayan harin, kamar yadda mai magana da yawun gwamnati ta faɗa. Shugaban Comoros Azali Assoumani ya samu rauni kadan a wani harin wuka da aka kai masa a ranar Juma'a, kakakin gwamnatin kasar ta ce an tsare maharin. Lamarin ya faru ne da misalin karfe biyu na ra...

Shugaba Azali Assoumani ya koma gida bayan harin, kamar yadda mai magana da yawun gwamnati ta faɗa. Shugaban Comoros Azali Assoumani ya samu rauni kadan a wani harin wuka da aka kai masa a ranar Juma'a, kakakin gwamnatin kasar ta ce an tsare maharin. Lamarin ya faru ne da misalin karfe biyu na rana. (1100 GMT) a Salimani Itsandra, wani gari da ke arewa da Moroni babban birnin ƙasar, kamar yadda wata majiya ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters. Mai magana da yawun gwamnatin kasar Fatima Ahamada ta shaida wa Reuters cewa, "An dan ji wa Shugaba Azali Assoumani rauni da wuka a yayin jana'izar wani babban shehin kasar. Ba a dai bayyana dalilin kai harin ba. Majiyar ta garin Salimani Itsandra ta ƙara da cewa maharin tsohon ɗan sanda ne mai kimanin shekaru 20 da haihuwa. A watan Mayu, an rantsar da Assoumani a wa'adi na hudu a kan karagar mulki, bayan zazzafan yaƙin neman zaɓe, wanda 'yan adawa suka yi zargin cewa cike yake da maguɗi.