Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

An jefi shugaban Kenya William Ruto da takalmi yana tsaka da jawabi

Wani gajeren bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda takalmin ya sami shugaban a kafaɗarsa ta hagu a lokacin da yake gudanar da jawabi. An jefi Shugaban Kenya William Ruto da takalmi a lokacin da yake jawabi ga dandazon jama’a a garin Kehancha da ke yammacin ƙasar a ranar Lahadi....

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:07
An jefi shugaban Kenya William Ruto da takalmi yana tsaka da jawabi
Em resumo

Wani gajeren bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda takalmin ya sami shugaban a kafaɗarsa ta hagu a lokacin da yake gudanar da jawabi. An jefi Shugaban Kenya William Ruto da takalmi a lokacin da yake jawabi ga dandazon jama’a a garin Kehancha da ke yammacin ƙasar a ranar Lahadi....

Wani gajeren bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda takalmin ya sami shugaban a kafaɗarsa ta hagu a lokacin da yake gudanar da jawabi. An jefi Shugaban Kenya William Ruto da takalmi a lokacin da yake jawabi ga dandazon jama’a a garin Kehancha da ke yammacin ƙasar a ranar Lahadi. Wani gajeren bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda takalmin ya sami shugaban a kafaɗarsa ta hagu a lokacin da yake gudanar da jawabi. Babu wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasar kan wannan lamari zuwa lokacin buga wannan labarin. Rangadi na kwana uku Ruto ya soma rangadinsa na kwana uku a garin Migori da ke yammacin Kenya. Migori na da nisan kilomita 370 daga Nairobi babban birnin ƙasar. Migory na da ƙawance sosai da ɓangaren ‘yan adawa, waɗanda ke ƙarƙashin jagorancin Raila Odinga, wanda bai samu nasara a kan Ruto ba a zaɓen Kenya da aka gudanar na shugaban ƙasa a shekarar 2022. Odinga, wanda ya riƙe muƙamin firaministan Kenya daga 2008 zuwa 2013 tuni ya cim ma yarjejeniyar haɗin kai da Shugaba Ruto. Gwamnatin shugaba Ruto da ke wa'adin mulkinta na farko na shekaru biyar, a lokuta da dama ta fuskanci adawa daga 'yan kasar Kenya, wadanda ke nuna rashin amincewarsu da ƙaruwar haraji da tsadar rayuwa, tun bayan hawan tsohon mataimakin shugaban kasar a kan karagar mulki a watan Satumban 2022.