Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

An haramta amfani da kwale-kwale marasa lasisi a Nijeriya domin inganta tsaro da kare rayuka

Matakin hakan na zuwa ne biyo bayan wasu munanan haɗurran kwale-kwalen ruwa da suka yi sanadiyar rasa rayukan mutane da dama a 'yan watannin baya-bayan nan a Nijeriya. Hukumar da ke kula da hanyoyin ruwa ta ƙasa a Nijeriya (NIWA) ta sanya dokar hana zirga-zirgar kwale-kwale waɗanda ba su da lasis...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:07
An haramta amfani da kwale-kwale marasa lasisi a Nijeriya domin inganta tsaro da kare rayuka
Kwa muhtasari

Matakin hakan na zuwa ne biyo bayan wasu munanan haɗurran kwale-kwalen ruwa da suka yi sanadiyar rasa rayukan mutane da dama a 'yan watannin baya-bayan nan a Nijeriya. Hukumar da ke kula da hanyoyin ruwa ta ƙasa a Nijeriya (NIWA) ta sanya dokar hana zirga-zirgar kwale-kwale waɗanda ba su da lasis...

Matakin hakan na zuwa ne biyo bayan wasu munanan haɗurran kwale-kwalen ruwa da suka yi sanadiyar rasa rayukan mutane da dama a 'yan watannin baya-bayan nan a Nijeriya. Hukumar da ke kula da hanyoyin ruwa ta ƙasa a Nijeriya (NIWA) ta sanya dokar hana zirga-zirgar kwale-kwale waɗanda ba su da lasisi da kuma lodi a wuraren da ba su da izinin yin hakan, a wani mataki na daƙile yawan haɗurran jiragen ruwa tare da kare rayukan al’umma a faɗin ƙasar. Babban daraktan hukumar ta NIWA, Bola Oyebamiji, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata. A cewarsa, daga yanzu ba za sake barin wani kwale-kwalen fasinja da ake biyan kuɗi ya yi lodi a tasha ko wurin da NIWA ba ta amince da shi ba. Hanyoyin ruwa masu hatsari: Dalilan da ke sa Nijeriya fuskantar hatsatsin jiragen ruwa a-kai-a-kai Kazalika ya jaddada cewa dole ne a bayyana sunayen dukkan kwale-kwale da kuma wuraren da suka yi lodi, yayin da su kuma masu gudanar da zirga-zirgarsu dole su samar da kuma tilasta yin amfani da rigunan kariya a ko yaushe. “NIWA ta sanya dokar hana yin lodi daga dukkan wuraren da ake yin lodin da ba sansu ba ko kuma ba su da izinin yin haka a faɗin ƙasar nan, ba za a bari wani kwale-kwale ya ɗauki fasinja ko ya yi lodi daga kowane wuri da NIWA ba ta amince ko kuma ta yi wa rajista ba,’’ a cewar Oyebamiji.