Yakin da Isra'ila ke yi da Falasɗinawa da suka yi wa ƙawanya a Gaza - wanda yanzu yake a rana ta 171 - ya kashe mutane aƙalla mutum 32,226 tare da jikkata mutum 74,518. 0342 GMT —Kwamitin Tsaro na MDD zai sake kaɗa ƙuri'a kan tsagaita wuta a Gaza Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya zai sake kaɗa ƙuri'a kan tsagaita wuta nan-take a Gaza, bayan Rasha da China sun hau kujerar-na-ƙi kan wani ƙuduri da Amurka ta gabatar. Kawunan mambobin kwamitin sun rabu game da yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba na 2023 bayan ƙungiyar Hamas ta kai mata harin ba-zata, inda suka amince da daftari biyu kawai daga cikin takwas, dukansu kan kai kayan jinƙai yankin. Amurka, wadda mamba ce ta dindindin a kwamitin, tana goyon bayan Isra'ila. 2300 GMT — An hana hukumar kula da Falasɗinawa ta MDD kai kayan agaji arewacin Gaza Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da ƴan gudun hijirar Falasɗinu ta bayyana cewa haƙiƙa Isra’ila ta hana ta kai kayan agaji a arewacin Gaza, inda ake fuskantar barazanar yunwa. "Duk da wannan bala'i da ke faruwa a kan idanuwanmu, hukumomin Isra'ila sun sanar da Majalisar Ɗinkin Duniya cewa ba za su sake amincewa da wani ayarin abinci na hukumar @UNRWA zuwa arewa ba," in ji Shugaban hukumar, Philippe Lazzarini a wani saƙo da ya wallafa a shafin X. "Wannan abin ban tsoro ne kuma ana yi ne da gayya don hana taimakon ceton rai a daidai lokacin da ake fama da tsananin yunwa wacce aka sabbaba ta da gangan." Daraktar sadarwa ta UNRWA Juliette Touma ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an yanke shawarar ne a wata ganawa da ta yi da jami'an sojin Isra'ila. Hakan ya biyo bayan hana jigilar ayarin motocin zuwa arewa a makon da ya gabata, inda aka aika musu batun hanin a rubuce. Ba a bayar da dalilin ɗaukar matakin ba, in ji Touma. Gaza na fuskantar mummunan yanayi na jinƙai sakamakon mummunan yakin da Isra'ila ke yi a yankin, wanda aka fara kusan watanni shida da suka gabata bayan farmakin ba-zata da Hamas ta kai a Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba. Tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023, fiye da mata 9,000 ne suka rasa rayukansu, sannan sama da mata 23,000 suka jikkata a ci gaba da hare-haren da sojojin Isra'ila ke kaiwa Gaza. / Hoto: Reuters / Photo: Reuters 1924 GMT — Jami'in Hamas ya ce an samu bambanci mai tsanani da Isra'ila a tattaunawar Gaza Akwai bambance-bambance masu zurfi tsakanin Hamas da Isra'ila a tattaunawar sulhun Gaza, kamar yadda wani jami'in kungiyar gwagwarmayar Falasdinu da ke da masaniya kan tattaunawar ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP. Jami'in ya ce "Akwai banbanci mai zurfi a cikin shawarwarin da ake yi tsakanin Hamas da Isra'ila ƴan mamaya, saboda maƙiya sun ɗauki sassaucin da ƙungiyar Hamas ke nunawa a matsayin rauni."
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
An hana hukumar kula da Falasɗinawa ta MDD kai kayan agaji arewacin Gaza
Yakin da Isra'ila ke yi da Falasɗinawa da suka yi wa ƙawanya a Gaza - wanda yanzu yake a rana ta 171 - ya kashe mutane aƙalla mutum 32,226 tare da jikkata mutum 74,518. 0342 GMT —Kwamitin Tsaro na MDD zai sake kaɗa ƙuri'a kan tsagaita wuta a Gaza Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya zai sake...

Yakin da Isra'ila ke yi da Falasɗinawa da suka yi wa ƙawanya a Gaza - wanda yanzu yake a rana ta 171 - ya kashe mutane aƙalla mutum 32,226 tare da jikkata mutum 74,518. 0342 GMT —Kwamitin Tsaro na MDD zai sake kaɗa ƙuri'a kan tsagaita wuta a Gaza Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya zai sake...
