Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

An gano wani babban kabari a Asibitin Al Shifa da ke Gaza — Rahoto

Gawawwakin da aka tono, waɗanda ba su gama ruɓewa ba, sun nuna cewa dakarun Isra'ila ba su jima da "kashe" mutanen ba, kuma alamu sun nuna cewa wasunsu marasa lafiya ne domin kuwa akwai bandeji a jikinsu, a cewar rahoton Al Jazeera. An gano wani babban kabari a Asibitin Al Shifa da ke Gaza, a cew...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:07
An gano wani babban kabari a Asibitin Al Shifa da ke Gaza — Rahoto
A taƙaice

Gawawwakin da aka tono, waɗanda ba su gama ruɓewa ba, sun nuna cewa dakarun Isra'ila ba su jima da "kashe" mutanen ba, kuma alamu sun nuna cewa wasunsu marasa lafiya ne domin kuwa akwai bandeji a jikinsu, a cewar rahoton Al Jazeera. An gano wani babban kabari a Asibitin Al Shifa da ke Gaza, a cew...

Gawawwakin da aka tono, waɗanda ba su gama ruɓewa ba, sun nuna cewa dakarun Isra'ila ba su jima da "kashe" mutanen ba, kuma alamu sun nuna cewa wasunsu marasa lafiya ne domin kuwa akwai bandeji a jikinsu, a cewar rahoton Al Jazeera. An gano wani babban kabari a Asibitin Al Shifa da ke Gaza, a cewar wani rahoton Al Jazeera Arabic . Ma'aikatar Lafiya ta Gaza da Rundunar Ƴan-kato-da-gora ne suka gano kabarin. Gidan talbijin ɗin da ke ƙasar Qatar ya ce an tono gawawwaki tara ranar Litinin a wajen asibitin da ke yammacin Gaza, sai dai jami'an kiwo lafiya sun dakatar da ci gaba da tono gawawwakin saboda fargabar da suke yi kan yiwuwar fuskantar hari daga jirage marasa matuƙa na Isra'ila da ke shawagi a yankin. Gawawwakin da aka tono, waɗanda ba su gama ruɓewa ba, sun nuna cewa dakarun Isra'ila ba su jima da "kashe" mutanen ba, kuma alamu sun nuna cewa wasunsu marasa lafiya ne domin kuwa akwai bandeji a jikinsu, a cewar rahoton. Dangin wasu daga cikin mutanen da aka tono gawawwakinsu sun gane ƴan'uwansu cikinsu har da wani dattijo da wata mace da kuma wani matashi ɗan kimanin shekara 20. Ma'aikatan asibitin da likitoci sun bayyana cewa an kashe mutane da dama a wajen babbar ƙofar shiga asibitin, wadda ake kira ƙofa mai lamba 80. Kazalika ma'aikatan lafiya sun ce sun ga lokacin da dakarun Isra'ila suka kashe wasu mutanen. A kwanakin baya ne dakarun Isra'ila suka janye daga Asibitin Al Shifa da ke Birnin Gaza bayan sun kwashe mako biyu suna mamaye shi, kuma sun ce sun yi ba-ta-kashi da mayaƙan Hamas a cikin asibitin da a baya ake kallo a matsayin babbar cibiyar kiwon lafiya ta Falasɗinawa.