Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

An ga watan azumin Ramadan a Nijeriya

Sarkin Musulmi na Nijeriya Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya ce ranar Litinin za ta kasance 1 ga watan watan Ramadan, don haka ya buƙaci duka ƴan Nijeriya su tashi da azumi. Sarkin Musulmi na Nijeriya Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya sanar da ganin watan azumin Ramadana a ƙasar. Ya bayya...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:07
An ga watan azumin Ramadan a Nijeriya
En bref

Sarkin Musulmi na Nijeriya Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya ce ranar Litinin za ta kasance 1 ga watan watan Ramadan, don haka ya buƙaci duka ƴan Nijeriya su tashi da azumi. Sarkin Musulmi na Nijeriya Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya sanar da ganin watan azumin Ramadana a ƙasar. Ya bayya...

Sarkin Musulmi na Nijeriya Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya ce ranar Litinin za ta kasance 1 ga watan watan Ramadan, don haka ya buƙaci duka ƴan Nijeriya su tashi da azumi. Sarkin Musulmi na Nijeriya Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya sanar da ganin watan azumin Ramadana a ƙasar. Ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya gabatar a fadarsa da ke Sokoto ranar Lahadi, kamar yadda kwamitin ganin wata na ƙasar ya fitar. https://t.co/r4ylbJTCqO — National Moonsighting Committee Nigeria (@moonsightingng) March 10, 2024 Ya ƙara da cewar ranar Litinin za ta kasance 1 ga watan watan Ramadan, don haka ya buƙaci duka ƴan ƙasar su tashi da azumi. Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya yi kira ga ƴan Nijeriya su yi wa ƙasarsu addu'a musamman game da matsalar rashin tsaro da tsadar rayuwa a wannan wata na Ramadana mai albarka. An ga watan Azumin Ramadana a Saudiyya Galibin ƙasashen duniya sun ga watan na Ramadana inda al'ummomin Musulman ƙasashen za su tashi da azumi. Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya mika gaisuwar fatan alheri ga Musulman duniya a yayin da ake soma azumin watan Ramadan mai albarka pic.twitter.com/2vAAGyHAHl — TRT Afrika Hausa (@trtafrikaHA) March 10, 2024 Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya mika gaisuwar fatan alheri ga Musulman duniya a yayin da ake soma azumin watan Ramadan mai albarka.