الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

An ceto ɗalibai biyar da aka yi garkuwa da su a Ekiti

Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta tabbatar da ceto ɗaliban da malamansu inda ta ce suna cikin ƙoshin lafiya. Rundunar yan sandan Nijeriya ta sanar da ceto wasu ɗalibai biyar da malamansu waɗanda aka sace a Jihar Ekiti. A wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Lahadi, ta ce an ceto ɗaliban da mal...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:07 ص
An ceto ɗalibai biyar da aka yi garkuwa da su a Ekiti
لمحة سريعة

Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta tabbatar da ceto ɗaliban da malamansu inda ta ce suna cikin ƙoshin lafiya. Rundunar yan sandan Nijeriya ta sanar da ceto wasu ɗalibai biyar da malamansu waɗanda aka sace a Jihar Ekiti. A wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Lahadi, ta ce an ceto ɗaliban da mal...

Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta tabbatar da ceto ɗaliban da malamansu inda ta ce suna cikin ƙoshin lafiya. Rundunar yan sandan Nijeriya ta sanar da ceto wasu ɗalibai biyar da malamansu waɗanda aka sace a Jihar Ekiti. A wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Lahadi, ta ce an ceto ɗaliban da malamansu ba tare da sun samu rauni ba. Lamarin ya faru ne a ranar Litinin 29 ga watan Janairun 2024 a lokacin da motar makaranta ke ƙoƙarin kai ɗaliban Eporo da ke Ekiti. “Muna jinjina da nuna jin daɗinmu kan ƙoƙarin gwamnati da jami’anmu na ƴan sanda da sauran jami’an tsaro waɗanda suka haɗa da Amotekun da bijilanti da mafarauta da ƴan uwa kan fahimtar da suka nuna da juriya,” kamar yadda ƴan sandan suka bayyana a sanarwar. Ekiti: We wish to inform the general public that the five school children, including their teachers, who were kidnapped on 29/01/2024 in Emure-Ekiti, have been rescued unhurt, today 4th February, 2024. We therefore commend and appreciate the efforts of the government, our… pic.twitter.com/no8EyhQBcS — Nigeria Police Force (@PoliceNG) February 4, 2024 Wannan na zuwa ne a yayin da ake samun hare-haren yan bindiga da masu garkuwa da mutane a sassan ƙasar. Rahotanni sun ce satar yaran da aka yi ya faru ne a daidai lokacin da ɓarayi suka kai hari kan wata mota da ke ɗake da wasu sarakunan gargajiya uku a tsakanin Oke-Ako da Ipao Ekiti da ke Ƙaramar Hukumar Ajoni.