Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

An binne tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura, jihar Katsina

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima da Firaministan Nijar Ali Lamine Zaine da tsohon shugaban Nijar Mahamadou Issoufou na daga dubban mutanen da suka halarci jana'izar a birnin Daura da yammacin Talata. An gudanar da jana’izar tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:07
An binne tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura, jihar Katsina
En bref

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima da Firaministan Nijar Ali Lamine Zaine da tsohon shugaban Nijar Mahamadou Issoufou na daga dubban mutanen da suka halarci jana'izar a birnin Daura da yammacin Talata. An gudanar da jana’izar tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a...

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima da Firaministan Nijar Ali Lamine Zaine da tsohon shugaban Nijar Mahamadou Issoufou na daga dubban mutanen da suka halarci jana'izar a birnin Daura da yammacin Talata. An gudanar da jana’izar tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a gidansa da ke birnin Daura na Jihar Katsina a arewacin ƙasar. An binne gawar marigayi Muhammadu Buhari ne da misalin karfe shida na yamma a agogon Nijeriya bayan kai ta Daura daga filin jirgin saman birnin Katsina. Buhari ya rasu ne a birnin Landan ranar Lahadi yana da shekaru 82 a duniya. Dubban mutane ne suka halarci jana’izar a karkashin sanya idon shugaban Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima da sauran manyan mutane daga ciki da wajen Nijeriya.