Shugaban Turkiyya kuma shugaban Jam'iyyar AK Recep Tayyip Erdogan ya gabatar da jawabi a wajen taron 'Yan Majalisar Dokoki ranar Laraba, inda ya yi tsokaci mai ƙarfi kan lamuran siyasa da shari'a na baya bayan nan. A jawabinsa, Erdogan ya jaddada cewa gwamnatinsa ba ta manta waɗanda suka yi yunƙurin kifar da su ta haramtacciyar hanya ba "Ba mu manta ba kuma ba za mu taɓa mantawa da wadanda suka yi yunƙurin kayar da mu ta haramtattun hanyoyi ba da kuma waɗanda suka yi ta fafatukar ganin sun jefa ƙasar nan cikin bala’i." Kazalika ya bayyana aniyar gwamnatinsa ta hukunta waɗanda suke yin ƙafar-ungulu ga harkokin tattalin arziki da bunƙasar ƙasar, yana mai cewa: "Za a hukunta dukkan masu wannan ƙafar-ungulu ga tattalin arzikin Turkiyya da walwala da zaman lafiyar ƙasa." Erdogan ya ce mambobin jam’iyyar CHP ne da kansu suka gabatar da shaidu game da mutanen da ake tuhuma da zargin cin hanci. Ya ce waɗannan mutane, waɗanda ba su gamsu da yadda ake raba kuɗaɗen haramun ba, su ne suka kai rahoton ɓarnar da ake yi ga jami’an tsaro, lamarin da ya kai ga shari’ar da ake yi yanzu. Erdogan ya ƙara da cewa an yi amfani da aka yi almubazzarancinsu ne wajen gudanar da ayyukan na ƙashin kai da kuma yin yaƙin neman zaɓe tare da tura wasu kuɗaɗen ga manyan ‘yan adawa. Da yake magana game da bincike kan cin hanci da ake yi wa Ƙananan Hukumomin Birnin Istanbul da sauran gundumomi, Erdogan ya ce: "An fahimci cewa ƙananan hukumomin da gundumomin sun shiga tsundum cikin harkokin cin hanci da sata da ƙwace." Ya ƙara da cewa idan aka bankaɗo girman cin hanci, waɗanda suka yi ɓarnar ba za su iya kallon fuskar iyalansu ba, ballantana al’umma. "Idan ana bankaɗo ainihi yadda lamarin ya faru (aka nuna manyan masu hannu a lamarin), ba za su iya kallon idanun iyalansu ba, bare al’umma." Erdogan ya kwatanta cin hancin da aka bankaɗo a ƙananan hukumomin Istanbul da ke ƙarƙashin jam’iyyar hamayya da wani wasan kwaikwayo mai dogon zango, yana mai cewa: "Idan kana so ka yi wasan kwaikwayo mai dogon zango a game da cin hanci na ƙananan hukumomin Istanbul na jam’iyyar CHP, za ka samu bayanai foye da waɗanda za ka samu idan za ka yi wasan kwanikwayon talbijin na Brazil." "A daina zanga-zanga a kan tituna" Da yake martani ga CHP, Erdogan soki matakin jam’iyyar na kare zarge-zargen cin hanci da kuma gudanar da zanga-zanga, inda ya yi kira a gare ta da ta bi hanyoyiyn shari’a. "Ko da kuwa saboda yaƙin cikin gida na CHP ne, an bankaɗo cin hancin da kuke yi. Ba za ku iya rufe hakan ba. Ku daina yin borin-kunya."
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
An bankaɗo cin hanci da rashawa na gwamnatin Istanbul ta Jam'iyyar CHP — Shugaba Erdogan
Shugaban Turkiyya kuma shugaban Jam'iyyar AK Recep Tayyip Erdogan ya gabatar da jawabi a wajen taron 'Yan Majalisar Dokoki ranar Laraba, inda ya yi tsokaci mai ƙarfi kan lamuran siyasa da shari'a na baya bayan nan. A jawabinsa, Erdogan ya jaddada cewa gwamnatinsa ba ta manta waɗanda suka yi yunƙu...
At a glance
Shugaban Turkiyya kuma shugaban Jam'iyyar AK Recep Tayyip Erdogan ya gabatar da jawabi a wajen taron 'Yan Majalisar Dokoki ranar Laraba, inda ya yi tsokaci mai ƙarfi kan lamuran siyasa da shari'a na baya bayan nan. A jawabinsa, Erdogan ya jaddada cewa gwamnatinsa ba ta manta waɗanda suka yi yunƙu...
