Ofishin Hadiza Bala Usman, mai bai wa shugaban Nijeriya shawara ta musamman kan tsare-tsare ne ya ƙaddamar da manhajar da zummar "fayyace" ayyukan da gwamnatin Bola Tinubu take yi ba tare da ɓoye-ɓoye ba. Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙaddamar da wata manhaja da za ta bai wa ƴan ƙasar damar bibiyar ayyukan da take yi don gani ko tana cika alƙawuran da ta ɗauka. Ofishin Hadiza Bala Usman, mai bai wa shugaban Nijeriya shawara ta musamman kan tsare-tsare ne ya ƙaddamar da manhajar da zummar "fayyace" ayyukan da gwamnatin Bola Tinubu take yi ba tare da ɓoye-ɓoye ba. Manhajar "za ta bai wa ƴan ƙasa damar bin diddigi da yin nazari da kuma yin tsokaci kan manufofi da ayyukan gwamnati," in ji Hadiza Bala. The Federal Government today launched the newly upgraded Citizens’ Delivery Tracker App. The app will empower the citizens to evaluate, track, monitor, report and give feedback on government's policies and programs, it will also enable citizens access to the Ministers… pic.twitter.com/Xqb4wkobkf — President Bola Ahmed Tinubu Media Centre (@PBATMediaCentre) April 8, 2024 Ta ƙara da cewa manhajar za ta bai wa mutane damar bin diddigin ayyukan da ministoci suke yi kamar yadda suka yi alƙawari tsakaninsu da shugaban ƙasa. Bola Tinubu: Alkawura bakwai da sabon shugaban Nijeriya ya yi wa 'yan kasar Za a iya sauke manhajar mai suna http://app.cdcu.gov.ng a Google Play Store kuma nan da wata guda za a iya sauke ta a Apple Store, in ji gwamnatin Nijeriya. "Abu mafi muhimmanci shi ne, wannan ne karo na farko da ƴan Nijeriya za su samu damar bin diddigin ayyukan dukkan ministoci abin da zai sa ƴan ƙasa su kasance wani ɓangare na masu ruwa da tsaki da ke auna ayyukan da gwamnati take yi," a cewar gwamnatin ta Nijeriya.
Arquivo de notícias
Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.
An ƙaddamar da manhaja don bin diddigin ayyukan gwamnatin Tinubu
Ofishin Hadiza Bala Usman, mai bai wa shugaban Nijeriya shawara ta musamman kan tsare-tsare ne ya ƙaddamar da manhajar da zummar "fayyace" ayyukan da gwamnatin Bola Tinubu take yi ba tare da ɓoye-ɓoye ba. Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙaddamar da wata manhaja da za ta bai wa ƴan ƙasar damar bibi...

Em resumo
Ofishin Hadiza Bala Usman, mai bai wa shugaban Nijeriya shawara ta musamman kan tsare-tsare ne ya ƙaddamar da manhajar da zummar "fayyace" ayyukan da gwamnatin Bola Tinubu take yi ba tare da ɓoye-ɓoye ba. Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙaddamar da wata manhaja da za ta bai wa ƴan ƙasar damar bibi...
