Jami'ai za su gana a Niamey babban birnin Jamhuriyar Nijar domin 'tsara yadda za a janye sojojin Amurka cikin "tsari da tsaro" daga ƙasar ta Afirka, in ji kakakin Pentagon Pat Ryder. Jami'an Amurka za su gana a yau Alhamis da mambobin gwamnatin Nijar kan janyewar sojojin Amurka daga kasar ta Afirka, in ji kakakin Ma'aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon. “A cewar ma’aikatar harkokin wajen Amurka, jakadiyar Amurka a Nijar Kathleen FitzGibbon da Manjo Janar Kenneth Ekman, daraktan tsare-tsare na rundunar sojojin Amurka a Afirka, za su gana da jami’an Kwamitin Tsaro na gida (CNSP) a ranar 25 ga Afrilu a Yamai, babban birnin Nijar don fara tattaunawa kan janyewar sojojin Amurka daga Nijar cikin tsari da aminci," kamar yadda Manjo Janar Pat Ryder ya fada a cikin wata sanarwa a ranar Laraba. Ryder ya ƙara da cewa, Christopher Maier, mataimakin sakataren tsaro na musamman kan ayyuka na musamman da rikice-rikicen da ba gagarumai ba, da Laftanar Janar Dagvin Anderson, daraktan dakarun hadin gwiwa, za su gudanar da tarukan bibiyar tattaunawar a babban birnin Yamai a mako mai zuwa. Amurka tana da sojoji kusan 1,100 a Nijar. Jamhuriyar Nijar dai na karkashin mulkin soji ne wanda ya hambarar da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum a watan Yulin da ya gabata, saboda tabarbarewar yanayin tsaro. Kasar Afirka ta Yamma ta soke yarjejeniyar soji da ta daɗe da ƙullawa da Washington a farkon watan Maris din wannan shekara, inda ta bayyana kasancewar dukkan sojojin Amurka da ‘yan kwangila a matsayinn waɗanda ke zaune a cikin ƙasar “ba bisa ƙa’ida ba” saboda “ba a amince da ita ta hanyar dimokuradiyya, kuma ta sanya sharuddan da ba su dace ba a Nijar, musamman ta fuskar rashin gaskiya kan ayyukan soji,” a cewar kakakin gwamnatin Nijar Amadou Abdramane. A lokacin gwamnatocin da suka gabata a Nijar, sojojin Amurka sun horar da sojojin Nijar kan yaƙi da ta'addanci.
Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.
Amurka za ta yi tattaunawar ƙeƙe-da-ƙeƙe da Nijar a kan tsarin janye dakarunta daga ƙasar — Pentagon
Jami'ai za su gana a Niamey babban birnin Jamhuriyar Nijar domin 'tsara yadda za a janye sojojin Amurka cikin "tsari da tsaro" daga ƙasar ta Afirka, in ji kakakin Pentagon Pat Ryder. Jami'an Amurka za su gana a yau Alhamis da mambobin gwamnatin Nijar kan janyewar sojojin Amurka daga kasar ta Afir...

Jami'ai za su gana a Niamey babban birnin Jamhuriyar Nijar domin 'tsara yadda za a janye sojojin Amurka cikin "tsari da tsaro" daga ƙasar ta Afirka, in ji kakakin Pentagon Pat Ryder. Jami'an Amurka za su gana a yau Alhamis da mambobin gwamnatin Nijar kan janyewar sojojin Amurka daga kasar ta Afir...
