"Yanzu haka Amurka tana da kimanin dakaru 300 a Nijar, kuma muna kan hanyar kwashe su cikin aminci ba tare da hargitsi ba nan da 15 ga watan Satumba," a cewar Mataimakiyar Kakakin Pentagon Sabrina Singh a hira da 'yan jarida. Amurka tana ci gaba da tattara komatsenta domin kwashe dukkan dakarunta kusan 1,000 daga jamhuriyar Nijar nan da ranar 15 ga watan Satumba, a cewar Ma'aikatar Tsaro ta Pentagon a ranar Litinin. "Yanzu haka Amurka tana da kimanin dakaru 300 a Nijar, kuma muna kan hanyar kwashe su cikin aminci ba tare da hargitsi ba nan da 15 ga watan Satumba," a cewar Mataimakiyar Kakakin Pentagon Sabrina Singh a hira da 'yan jarida. Singh ta ce Amurka ta kammala kwashe dakarunta daga sansanin sojojin sama na Air Base 101 da ke Yamai ranar 7 ga watan Yuli. A watan Maris Nijar ta kawo ƙarshen dangantakar soji da Washington, inda ta bayyana zaman dakarun Amurka a ƙasar a matsayin "haramtacce" saboda Amurka "tana ƙaƙaba mana sharuɗɗan da ba su dace da dimokuraɗiyya ba kua ba su da gurbi a Nijar," kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin sojin ƙasar Amadou Abdramane ya bayyana.
Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.
Amurka tana da dakaru kusan 300 a Jamhuriyar Nijar: Pentagon
"Yanzu haka Amurka tana da kimanin dakaru 300 a Nijar, kuma muna kan hanyar kwashe su cikin aminci ba tare da hargitsi ba nan da 15 ga watan Satumba," a cewar Mataimakiyar Kakakin Pentagon Sabrina Singh a hira da 'yan jarida. Amurka tana ci gaba da tattara komatsenta domin kwashe dukkan dakarunta...