Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

Amurka ta sake ƙin yi wa fursunonin da suka tsira da cin zarafin gidan yarin Abu Ghraib adalci

Rashin yanke hukunci ya kafa mumunan tarihi a rikice-rikicen da duniya ke fama da shi, ciki har da cin zarafin Falasdinawa a gidajen yarin Isra'ila da kuma fursunonin Ukraine da ke tsara a hannun jami'an Rasha. Daga Hamzah Rifaat Shekaru 20 kenan da mumunar labarin cin zarafin da ake yi a gidan y...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:07
Amurka ta sake ƙin yi wa fursunonin da suka tsira da cin zarafin gidan yarin Abu Ghraib adalci
Em resumo

Rashin yanke hukunci ya kafa mumunan tarihi a rikice-rikicen da duniya ke fama da shi, ciki har da cin zarafin Falasdinawa a gidajen yarin Isra'ila da kuma fursunonin Ukraine da ke tsara a hannun jami'an Rasha. Daga Hamzah Rifaat Shekaru 20 kenan da mumunar labarin cin zarafin da ake yi a gidan y...

Rashin yanke hukunci ya kafa mumunan tarihi a rikice-rikicen da duniya ke fama da shi, ciki har da cin zarafin Falasdinawa a gidajen yarin Isra'ila da kuma fursunonin Ukraine da ke tsara a hannun jami'an Rasha. Daga Hamzah Rifaat Shekaru 20 kenan da mumunar labarin cin zarafin da ake yi a gidan yarin Abu Ghraib. Hotunan ban tausayi da tashin hankali da kuma rashin imani da mutunta ɗan adam na yadda sojojin Amurka ke cin zarafi da kuma wulakanta fursunonin gidan yarin Abu Ghraib da ke kasar Iraki sun matukar taɗa jijiyoyin wuta a duniya. An yi ta sukar Sakataren Tsaron kasar na lokacin Donald Rumsfeld saboda sa ido da kuma ƙarfafa ayyukan cin zarafi kan fursunoni a karkashin gwamnatin shugaba George W. Bush na Amurka. Har yanzu an gagara samar wa mutanen da lamarin ya shafa adalci. Lauyoyi uku da suka gabatar da ƙara sun shafe tsawon lokaci suna gwagwarmaya kan shari'ar, kana a karshe suka samu zama a kotu a watan da ya wuce bayan wata ƙarar aka shigar kan Cibiyar Nazarin Tattalin Arziki ta Virginia (CACI). Sun yi zargin cewa ma'aikatan da ke aiki da sojojin Amurka a lokacin sun aikata munanan cin zarafi a gidan yarin. A judge declared a mistrial Thursday after a jury said it was deadlocked and could not reach a verdict in the trial of a military contractor accused of contributing to the abuse of detainees at the Abu Ghraib Prison in Iraq. https://t.co/ZKSGwCaNBj — WTOP (@WTOP) May 2, 2024 Sai dai zaman katun ya gamu da cikas, bayan da alkalin da ke jagorantar shari'ar ya bayyana cewa shari'ar ba ta kammalu ba. Wannan rashin adalci ne tsantsa. Abun da faru Lamarin ya soma ne bayan mamayar Amurka na shekarar 2003 a Iraki don hambarar da gwamnatin Saddam Hussein. A 2004, shirin labaran Minti 60 da gidan talabijin din Amurka ya ɗauka, ya bayyana hotunan 'yan Iraqi maza da jami'an Amurka ke cin zarafinsu ta hanyar duka da azabtarwa a gidan yarin Abu Ghairb. Kazalika lamarin ya biyo bayan watanni 13 da kawanya da kuma mamayar Amurka a Iraki. What made torture at Abu Ghraib possible was not just the individuals willing to enact brutality, but the rendering of Muslims and Arabs as a “torturable class.” via @Dr_Maha_Hilal https://t.co/e2K163nqK1 — Mobashra (@mobbiemobes) April 29, 2024 Wannan al'amari ya zama abin kunya da misali ga mulkin mallaka da munafurcin da Amurka ke nuna wa wajen ɗaukaka kanta a matsayin abin da ake kira tushen manufar ‘yantar da ƙasar Iraki, kafin a gano sojojinta na dukan fursunonin Iraqi tare da cin zarafinsu. A cewar kungiyar agaji ta Red Cross, kashi 70 zuwa 90 cikin 100 na fursunonin Abu Ghraib da aka tsare, wadanda ba su ji ba ba su gani ba ne aka kama su bisa kuskure kana suka fada kuncin rayuwa a azaba da kuma cin zarafi daga hannun jami'an sojin Amurka. Rahoton ICRC na 2004 ya bayyana cewa akwai tarin misalai na cin zarafi a Abu Ghraib waɗanda suka keta Yarjejeniyar Geneva, gami da zagi da wulakanci da kuma azabtarwar fitar hankali daga masu tambayoyi. Sakamakon binciken da hotuna da rahotanni da aka fitar sun haifar da ce-ce-ku-ce a fadin duniya wanda ya kai ga Majalisar Dinkin Duniya. A lokacin, Mukaddashin Babban Kwamishinan Kare Hakkokin ɗan Adam Bertrand Ramicharan ya ba da bayyana cewa mumunar ayyukan cin zarafin fursunoni a Abu Ghraib ka iya zama laifin yaki. "This will not be the final word; what happened in Abu Ghraib is engraved into our memories and will never be forgotten in history," one plaintiff vowed after a Virginia jury deadlocked in the torture case against mercenary firm CACI. https://t.co/XmzIwoMaME — Common Dreams (@commondreams) May 2, 2024 An shigar da karar farko kan CACI a shekarar 2008 kana aka jinkirtar da shari'ar har zuwa shekaru 15 saboda takaddamar doka da korar da kamfanin ya yi kan zargin cewa jami'an suna da rigar kariya kana doka ta kare su a yayin da suke aiki a matsayin sojojin Amurka. Bayan shekara daya, wata kotun daukaka kara ta Amurka ta yi watsi da karar da wasu 'yan Iraki mutum 250 suka shigar, wadanda aka azabtar da su a gidan yarin Abu Ghraib bisa ga dogaro kan dokar bincike da ake kira da "battlefield preemption." Duk da tsanani da girman cin zarafin da aka aiwatar, wasu kananan jami’an sojoji ne kawai aka gurfanar da su gaban kotu. Kafa misalai masu muni Rashin ɗaukar nauyi ko alhaki na zama babbar matsala. Shari'ar 2024 na zuwa ne a daidai lokacin da duniya ke ganin manya riƙice-riƙecen da cin zarafi masu muni. Hakan ya kafa babbar hujja mai haɗari kan cewa za a ci gaba da cin zarafin fursunoni saboda rashin adalci da kariya ga waɗanda lamarin ya shafa. Hakan ya hada da cin zarafin Falasdinawa a gidajen yarin isra'ila da kuma fursunonin Ukraine da jami'an Rasha ke yi. "It's like a hell." A newly released Palestinian prisoner who has been arrested by the Israeli army from Nasser Hospital in Khan Yunis describes the horrors he experienced during his 60-day ordeal in Israeli imprisonment. pic.twitter.com/5SDI826Rm9 — Quds News Network (@QudsNen) May 4, 2024 Dubban fursunonin Ukraine ne ake tsare da su a gidajen yarin Rasha tun lokacin da aka fara kai farmakin a shekarar 2022, inda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, jami'an Rashan sun azabtar da su da wutar lantarki da aiwatar da hukuncin duka mai tsanani da daukar tsawon lokaci wurin azabtarwa har ma da barazanar kisa. Haka zalika, likitocin Isra'ila sun bayyana mummunan yanayin da fursunonin Falasdinawan daga Gaza suke ciki a cibiyoyin da ake tsare da su na wucin gadi, Yanayin da ya hada da kulle a kowane lokaci tare da rufe musu idanuwa da kuma fuskantar azabatarwar jiki da wulakanci da kuma cin zarafi. "Iraqi torture survivors who have pursued the lawsuit for nearly 16 years intend to seek another trial." https://t.co/QHDgwaA3MF — Natylie Baldwin (@natyliesb) May 3, 2024 Su ne Suhail Najim Abdullah Al Shimari, Salah Al-Ejaili da As'ad Al-Zuba'e. Al-Ejaili ɗan jarida ne kafin sojojin Amurka su kama shi kuma ya shaida cewar an yi masa mugun duka, da ɗaure shi da kuma tsare shi cikin yanayi na rashin fahimta duk da cewa ba a tuhume shi da wani laifi ba. Masu shigar da ƙara sun ce sun sha irin wannan cin zarafi. An fara shari'ar da masu shigar da ƙara suna jayayya cewa CACI na da alhakin cin zarafi duk da rashin iya tabbatar da cewa masu binciken dan kwangilar suna da alhakin cin zarafin fursunoni kai tsaye. Shaidu sun zo ta hanyar shaidar wadanda abin ya shafa da wasu janar-janar na sojan Amurka biyu da suka yi ritaya wadanda suka rubuta cin zarafi a Abu Ghraib tare da alakanta CACI da shi. A cikin rana ta takwas na muhawara duk da haka, alkali ya ayyana shari'ar da ba ta dace ba bayan da alkalai na mutane takwas a Alexandria suka kasa yarda da yanke hukunci. Wannan ya zo ne kai tsaye bayan CACI ta yi jayayya cewa bai kamata ya zama alhakin ayyukan da Sojojin Amurka suka aikata ba kuma ya kamata a rataya alhakin gwamnati a maimakon haka. Akwai yuwuwar a sake zaman shari'ar, amma matakin rashin kammala shari'ar da alkalin ya nuna cewa ba za a sake samarwa fursunonin Abu Ghaib adalci ba lamarin da ya girgiza duniya ya kuma keta yarjejeniyoyin Geneva da tona asirin Amurka da munafuncinta. Shin za a taɓa yin adalci? Hamzah Rifaat na da shaidar digiri a fannin Nazarin Zaman Lafiya da rikice-rikice a Islamabad da Pakistan da kuma Harkokin duniya da Diflomasiya daga jami'ar Bandaranaike da ke Colombo na ƙasar Sri Lanka. Hamzah ya taba kasancewa wakilin Kudancin Asiya a Cibiyar Stimson da ke Washington, DC a cikin 2016. Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubucin ya yi daidai da ra'ayi ko ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika ba.