Kasashe goma sha uku mambobin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da daftarin dokar da Hadaddiyar Daular Larabawa ta gabatar. Birtaniya ta ki kada kuri'a yayin da Amurka ta ki amincewa da kudurin. Amurka ta yi fatali da kudurin da aka gabatar ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya wanda zai bayar da dama a tsagaita wuta a hare-haren da Isra'ila take kaiwa Gaza da aka mamaye, abin da ya mayar da ita saniyar-ware a fannin diflomasiyya inda take kare muradun Isra'ila. Mataimakin Wakilin Amurka a MDD, Robert Wood, ranar Juma'a ya ce kudurin dokar "bai yi kama da gaskiya ba" kuma "ba zai samar da mafita kan abin da ke faruwa a kasa ba." Ya ce tsagaita wuta zai bai wa Hamas damar ci gaba da gudanar da mulkin Gaza kuma "zai dasa damba ta yaki a nan gaba" — wannan shi ne ra'ayin Isra'ila abin da ya sa take so n sake mamaye yankin na Falasdinu. Kasashe goma sha uku mambobin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da daftarin dokar da Hadaddiyar Daular Larabawa ta gabatar. Birtaniya ta ki kada kuri'a yayin da Amurka ta ki amincewa da kudurin. Wannan shi ne karo na 47 da Amurka take hawa kujerar-na-ki kan batun da ya shafi Isra'ila tun daga 1945. An kada kuri'ar ne bayan Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya dauki wani mataki na ba-safai ba ranar Laraba inda a hukumance ya gargadi mambobi 15 na Kwamitin game da barazanar da duniya ke fuskanta daga yakin na Isra'ila. Daftarin, wanda kasashe akalla 97 mambobin MDD suka dauki nauyinsa, ya yi kira ga dukkan bangarorin da ke rikici su yi biyayya ga dokokin kasashen duniya na yaki, musamman kudurin na so a kare fararen-hula da tsagaita wuta sannan ya yi kira ga ga shugaban MDD ya tabbatar an tsagaita wuta.
Архив новостей
В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.
Amurka ta ki amincewa da kudurin da ke so a tsagaita wuta a hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza
Kasashe goma sha uku mambobin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da daftarin dokar da Hadaddiyar Daular Larabawa ta gabatar. Birtaniya ta ki kada kuri'a yayin da Amurka ta ki amincewa da kudurin. Amurka ta yi fatali da kudurin da aka gabatar ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin...

Кратко
Kasashe goma sha uku mambobin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da daftarin dokar da Hadaddiyar Daular Larabawa ta gabatar. Birtaniya ta ki kada kuri'a yayin da Amurka ta ki amincewa da kudurin. Amurka ta yi fatali da kudurin da aka gabatar ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin...
