Amurka na yunƙurin tabbatar da wakilcin din-din-din ga ƙasashen Afirka biyu da karba-karba ga ƙananan tsibirai da ƙarin goyon bayan da take bai wa India da Japan da Jamus don su zama mambobin din-din-din a Kwamitin Tsaro na Majlisar Dinkin Duniya. Amurka na goyon bayan bayar da kujerun din-din-din a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ga ƙasashen Afirka biyu, da kujera ɗaya ta karɓa-karɓa ga ƙasashen dake ƙananan tsibirai, kamar yadda Jakadiyar Amurka a MDD Linda Thomas-Greenfield za ta bayyana a ranar Alhams ɗin nan. Thomas-Greenfield ta faɗa wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa tana fatan sanarwar za ta "kara ƙarfafa wannan manufa ta hanyar da za a iya kawo sauyi a Kwamitin Tsaro a nan gaba," inda ta kuma ce wannan na daga manufofin Shugaba Joe Biden. Ƙasashe masu tasowa sun jima suna neman a ba su kujerun din-din-din a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, kwamiti mafi ƙarfi a Majalisar. Amma bayan shekaru ana tattaunawa kan yin sauye-sauye, an kasa cimma matsaya kuma ba a da tabbacin ko goyon bayan Amurka na iya ya janyo ɗaukar wannan mataki ba. Kafin bayar da sanarwar a Kwamitin Harkokin Kasashen Waje a New York a ranar Alhamis, Thomas Greenfield ta yi karin haske ga Reuters cewa Washington ba ta goyon bayan ƙara yawan kasashen da suke da karfin zartar da hukunci na hawa kujerar na-ƙi sama da biyar a suke da shi a yanzu. Kwamitin Tsaron na da alhakin samar da tsaro da zaman lafiya a duniya, kuma yana da karfin saka takunkumai da hana saye ko mallakar makamai, kuma yana bayar da umarnin amfani da ƙarfi. A lokacin da aka kafa Majalisar Ɗinkin Duniya a 1945, Kwamitin Tsaro na Majalisar na da mambobi 11. An kara yawan su zuwa 15 a shekarar 1965, 10 zaɓaɓɓu dake karba-karba na shekru biyu-biyu, da guda biyar da ke da karfin zartar da ikon hawa kujerar na-ƙi; Rasha da China da Faransa daAmurka da kuma Birtaniya. Batun halasci Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres na goyon bayan kawo sauyi a Kwamitin Tsaron. "Kana da Kwamitin Tsaro da ya samu kansa a irin halin da aka shiga bayan Yaƙin Duniya na Biyu... wannan na da matsalar halasci, wannan na da matsalar tasiri, yana bukatar yi masa sauye-sauye," kamar yadda Guterres ya faɗa wa Reuters a ranar Laraba. Ana yin duk wani sauyi na zama mamba a Kwamitin Tsaro ta hanyar kwaskwarima ga dokar da ta kafa Majalisar Dinkin Duniya. Wannan na buƙatar amincewar kashi biyu cikin uku na Babban Zauren Majalisar, ciki har da mambobin din-din-din masu hawa kujerar na-ƙi su biyar. A cikin sama da shekaru 10 Babban Zauren MDD da ke da mambobi 193 kowace shekara na tattaunawa kan kawo sauyi da yin gyara a Kwamitin Tsaron. Amma a shekarun baya-bayan nan an yi ta samun ɗaga murya daga ƙasashe saboda yadda ƙasashen da suke adawa da juna suke cin karo kan wasu batutuwa, musamman da a yanzu ƙasar da ke da karfin hawa kujerar na-ƙi Rasha ta kai hari Ukraine. Thomas-Greenfield za ta bayyana a ranar Alhamis cewa,"Mafi yawan tattaunawa kan sauye-sauye a Kwamitin Tsaro na karewa ne a baka kawai," kamar yadda Reuters ta gani a jawabin da aka tanada za ta yi, wanda zai bayyana goyon bayan Washington ga fara tattaunawa kan rubuta wani daftari na gyara kan dokar da ta kafa majalisar, don a ƙara yawan kasashe a Kwamitin. Thomas Greenfield ta faɗa wa Reuters cewa ba za ta iya cewa ga lokacin da za a ɗauka ba kafin Babban Zauren ya amince da wannan mataki. A kowacce shekara Babban Zauren MDD yana zaɓar sabbin mambobi biyar daga nahiyoyi daban-daban a matsayin mambobin shekaru biyu a Kwamitin Tsaro na MDD. A yanzu Afirka na da kujeru uku na karɓa-karɓa tsakanin ƙasashen nahiyar. "Matsalar ita ce, waɗannan ƙasashe mambobin din-din-din ba sa bai wa kasashen Afirka sukunin bayar da cikakkiyar damar amfana da ilimi da muryoyinsu a ayyukan Kwamitin ... a koyaushe su jagoranci warware matsalolin da ke damun mu gaba ɗaya - waɗanda kuma ke damun wasu yankunan na Afirka," Thomas-Greenfield za ta bayyana a wajabinta. Za kuma ta bayyana cewa ƙasashen kananan tsibirai sun cancanci zama mambobin da za su dinga yin karɓa-karɓa saboda suna bayar da "kyawawan shawarwari kan batutuwan tsaro da zaman lafiyar duniya, ciki har da tasirin sauyin yanayi."
Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.
Amurka na goyon bayan bai wa ƙasashen Afirka mambobin din-din-din marasa ƙarfin kujerar na-ƙi a Kwamitin Tsaro na MDD
Amurka na yunƙurin tabbatar da wakilcin din-din-din ga ƙasashen Afirka biyu da karba-karba ga ƙananan tsibirai da ƙarin goyon bayan da take bai wa India da Japan da Jamus don su zama mambobin din-din-din a Kwamitin Tsaro na Majlisar Dinkin Duniya. Amurka na goyon bayan bayar da kujerun din-din-di...

Amurka na yunƙurin tabbatar da wakilcin din-din-din ga ƙasashen Afirka biyu da karba-karba ga ƙananan tsibirai da ƙarin goyon bayan da take bai wa India da Japan da Jamus don su zama mambobin din-din-din a Kwamitin Tsaro na Majlisar Dinkin Duniya. Amurka na goyon bayan bayar da kujerun din-din-di...
