Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

Amurka da Birtaniya sun kaddamar da hare-hare kan 'yan tawayen Houthis na Yemen

Wasu jami'ai na kungiyar Houthi sun ce "Amurkawa da Masu kishin Yahudawa da Birtaniya" sun kaddamar da jerin hare-hare a kansu, suna masu cewa su ma sun kaddamar da hare-haren ramuwar gayya. Sojojin Amurka da na Birtaniya sun kai gomman a yankunan 'yan tawayen Houthi na Yemen, inda suka yi amfani...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:07
Amurka da Birtaniya sun kaddamar da hare-hare kan 'yan tawayen Houthis na Yemen
Bu haberde ne var?

Wasu jami'ai na kungiyar Houthi sun ce "Amurkawa da Masu kishin Yahudawa da Birtaniya" sun kaddamar da jerin hare-hare a kansu, suna masu cewa su ma sun kaddamar da hare-haren ramuwar gayya. Sojojin Amurka da na Birtaniya sun kai gomman a yankunan 'yan tawayen Houthi na Yemen, inda suka yi amfani...

Wasu jami'ai na kungiyar Houthi sun ce "Amurkawa da Masu kishin Yahudawa da Birtaniya" sun kaddamar da jerin hare-hare a kansu, suna masu cewa su ma sun kaddamar da hare-haren ramuwar gayya. Sojojin Amurka da na Birtaniya sun kai gomman a yankunan 'yan tawayen Houthi na Yemen, inda suka yi amfani da jiragen ruwan yaki wurin harba makamai masu linzami samfuran Tomahawk tare da jiragen yaki. Sojojin sun kai hare-hare a wuraren da suka hada da ma'ajiyar makamai da na'urorin kare hare-hare ta sama, a cewar jami'an gwamnatin Amurka ranar Juma'a da safe. Wadannan hare-hare su ne karon farko da Amurka ta yi martani kan 'yan tawayen Houthis wadanda suka dade suna yin amfani da jirage marasa matuka da makamai masu linzami wajen kai hari kan jiragen ruwa na daukar kaya da ke zuwa Isra'ila tun lokacin da aka kaddamar da hare-hare a Gaza. Shugaban Amurka Joe Biden ya ce hare-haren da suka kai Yemen sun nuna cewa kasarsa da kawayenta ba za su "lamunci" hare-haren da 'yan tawayen Houthi suke kai wa jiragen ruwansu ba. A wata sanarwa da ya fitar, Biden ya ce a karon farko sun yi amfani da makamai masu linzami na ruwa wajen kai hare-hare kan 'yan tawayen Houthi ne domin yin raddi game da jerin hare-haren da suke kai wa jiragen ruwa da ke wucewa ta Bahar Maliya. A gefe guda, shugaban Houthi Ali al-Qahoum ya ce sun kaddamar da hare-hare kan jiragen yakin Amurka da Birtaniya da ke Bahar Maliya domin yin martani kan hare-haren da aka kai musu. "Amurkawa da Masu kishin Yahudawa da Birtaniya da ke yaki da Yemen sun kaddamar da jerin hare-hare a babban birnin, Sanaa, da yankin Hudaida da Saada, da kuma Dhamar," a cewar wani jami'in Houthi Abdul Qader al Mortada a sakon da ya wallafa a shafin X. Wakilan kamfanin dillancin labarai na Associated Press journalists a Sanaa sun ji kara hudu ta fashewar wasu abbuwa amma ba su ga alamar jiragen yaki ba.