Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Ambaliyar ruwa ta shafi fiye da mutum 110,346 — Gwamnatin Nijar

Kanar-Manjo Salissou Mahaman Salissou ya bayyana cewa ambaliyar ruwa ta bana ta shafi unguwanni 551 da ƙananan hukumomi 95 da kuma iyalai 15,177 a faɗin ƙasar Nijar. Aƙalla mutum 110,346 ne ambaliyar ruwa ta shafa a cikin jihohi takwas na Jamhuriyar Nijar zuwa ranar 28 ga watan Agusta, a cewar gw...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:07
Ambaliyar ruwa ta shafi fiye da mutum 110,346 — Gwamnatin Nijar
At a glance

Kanar-Manjo Salissou Mahaman Salissou ya bayyana cewa ambaliyar ruwa ta bana ta shafi unguwanni 551 da ƙananan hukumomi 95 da kuma iyalai 15,177 a faɗin ƙasar Nijar. Aƙalla mutum 110,346 ne ambaliyar ruwa ta shafa a cikin jihohi takwas na Jamhuriyar Nijar zuwa ranar 28 ga watan Agusta, a cewar gw...

Kanar-Manjo Salissou Mahaman Salissou ya bayyana cewa ambaliyar ruwa ta bana ta shafi unguwanni 551 da ƙananan hukumomi 95 da kuma iyalai 15,177 a faɗin ƙasar Nijar. Aƙalla mutum 110,346 ne ambaliyar ruwa ta shafa a cikin jihohi takwas na Jamhuriyar Nijar zuwa ranar 28 ga watan Agusta, a cewar gwamnatin ƙasar. Ministan kayayyaki da ababen more rayuwa na ƙasar kuma mataimakin shugaban kwamitin hana ambaliya na Nijar, Kanal-Manjo, Salissou Mahaman Salissou, ne ya bayyana wannan a lokacin da yake jagorantar zaman kwamitin a Yamai ranar Alhamis. Kanar-Manjo Salissou Mahaman Salissou ya bayyana cewa ambaliyar ruwa ta bana ta shafi unguwanni 551 da ƙananan hukumomi 95 da kuma iyalai 15,177 a faɗin ƙasar Nijar. Zaman kwamitin ya yi nazari game da irin gidajen da suka kamata a gina wa waɗanda ambaliyar ta fi shafa.