Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 23 a Jamruriyar Nijar

A sanarwar da ta fitar a taron, GNSP ta ce ambaliyar ruwa ta rusa gidaje 361. Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa ambaliyar ruwa ta kashe mutum 23 tare da jikkata 21 yayin da ta raba mutum 42,000 da gidajensu. Kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ruwaito cewa hukumar kwana-kwana ta ƙasar (GNSP...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:07
Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 23 a Jamruriyar Nijar
En bref

A sanarwar da ta fitar a taron, GNSP ta ce ambaliyar ruwa ta rusa gidaje 361. Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa ambaliyar ruwa ta kashe mutum 23 tare da jikkata 21 yayin da ta raba mutum 42,000 da gidajensu. Kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ruwaito cewa hukumar kwana-kwana ta ƙasar (GNSP...

A sanarwar da ta fitar a taron, GNSP ta ce ambaliyar ruwa ta rusa gidaje 361. Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa ambaliyar ruwa ta kashe mutum 23 tare da jikkata 21 yayin da ta raba mutum 42,000 da gidajensu. Kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ruwaito cewa hukumar kwana-kwana ta ƙasar (GNSP) ce ta bayyana hakan a wani taron maneman labarai da ta gabatar ranar Alhamis. A sanarwar da ta fitar a taron, GNSP ta ce ambaliya ta rusa gidaje 361. Sai dai ba ta faɗi lokacin da lamarin ya faru ba. Kazalika GNSP ta tuna wa mutane shawarwarin da ta bayar a baya game da matakan da ya kamata a ɗauka wajen kauce wa hatsarin ambaliyar musamman ƙaurace wa tsallake gadajojin da ruwa ya rufe da kuma barin wuraren ambaliya da kuma rashin zama a gidaje masu rauni. Ta kuma gargaɗi mutane game da fakewa ƙarƙshin bishiyoyi da toshe magudanan ruwa da linƙaya a a cikin ƙududdufi da kuma tono bayan ayi ruwa