Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Ambaliya ta halaka aƙalla mutum 47 da kuma raba dubbai da gidajensu a Nijar

Dubban mutane ne ambaliya ta raba da gidajensu tare da kashe dabbobi, in ji hukumomin ƙasar. Ambaliya ta kashe aƙalla mutum 47 tare da raba fiye da mutum 56,000 da gidajensu a Jamhuriyar Nijar, in ji hukumomin ƙasar a ranar Laraba. Ambaliyar ta shafi gidaje 7,754 a cikin unguwanni da ƙauyuka 339...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:07
Ambaliya ta halaka aƙalla mutum 47 da kuma raba dubbai da gidajensu a Nijar
De un vistazo

Dubban mutane ne ambaliya ta raba da gidajensu tare da kashe dabbobi, in ji hukumomin ƙasar. Ambaliya ta kashe aƙalla mutum 47 tare da raba fiye da mutum 56,000 da gidajensu a Jamhuriyar Nijar, in ji hukumomin ƙasar a ranar Laraba. Ambaliyar ta shafi gidaje 7,754 a cikin unguwanni da ƙauyuka 339...

Dubban mutane ne ambaliya ta raba da gidajensu tare da kashe dabbobi, in ji hukumomin ƙasar. Ambaliya ta kashe aƙalla mutum 47 tare da raba fiye da mutum 56,000 da gidajensu a Jamhuriyar Nijar, in ji hukumomin ƙasar a ranar Laraba. Ambaliyar ta shafi gidaje 7,754 a cikin unguwanni da ƙauyuka 339 , in ji hukumar tsaron fararen hular ƙasar. “Wasu mutum 30 sun mutu bayan gidajensu sun rushe yayin da mutum 17 suka nutse a ruwa. “Kazalika ambaliyar ta raunata mutum 70 ta kuma haddasa mutuwar dabbobi 257,” in ji hukumar. Kwamiti na ƙasa da aka ɗora wa alhakin hana ambliya ya ce ya fara raba tallafin abinci ga iyalai 3,776.