Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Alkalin Alkalan Nijeriya ya kira manyan alkalan Kotun Tarayya da Jiha kan dambarwar Masarautar Kano

Alkalin Alkalan Nijeriya Mai Shari’a Olukayode Ariwoola ya yi sammacin manyan alkalan Babbar Kotun Tarayya da ta na Jihar Kano kan ba da dokoki masu karo da juna da suka shafi dambawar Masarautar Kano. Alkalin Alkalan Nijeriya Mai Shari’a Olukayode Ariwoola ya yi sammacin manyan alkalan Babbar Ko...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:07
Alkalin Alkalan Nijeriya ya kira manyan alkalan Kotun Tarayya da Jiha kan dambarwar Masarautar Kano
En bref

Alkalin Alkalan Nijeriya Mai Shari’a Olukayode Ariwoola ya yi sammacin manyan alkalan Babbar Kotun Tarayya da ta na Jihar Kano kan ba da dokoki masu karo da juna da suka shafi dambawar Masarautar Kano. Alkalin Alkalan Nijeriya Mai Shari’a Olukayode Ariwoola ya yi sammacin manyan alkalan Babbar Ko...

Alkalin Alkalan Nijeriya Mai Shari’a Olukayode Ariwoola ya yi sammacin manyan alkalan Babbar Kotun Tarayya da ta na Jihar Kano kan ba da dokoki masu karo da juna da suka shafi dambawar Masarautar Kano. Alkalin Alkalan Nijeriya Mai Shari’a Olukayode Ariwoola ya yi sammacin manyan alkalan Babbar Kotun Tarayya da ta na Jihar Kano kan ba da dokoki masu karo da juna da suka shafi dambawar Masarautar Kano. Tun a makon da ya gabata ne ake ta dambarwa a kan Masarautar Kano bayan da gwamnatin jihar ta sauke sarakunan biyar da rushe masarautu hudu sannan ta mayar da Sarki Muhammadu Sanusi II. Jim kaɗan bayan hakan ne sai Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a S. A. Amobeda ta bayar da wani uamrni na fitar da Sarki Muhammadu Sanusi II daga cikin Fadar Kofar Kudu, tare da mayar da Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero cikinta. Mai Shari’a Amobeda ya ce “An ba da umarnin wucin gadi da ya hana wadanda ake ƙara gayyatar ko kama ko tsare ko barazana ko tsoratarwa ko musguna wa wanda ya shigar da ƙarar ko kuma tauye masa hakkinsa”. Ya kara da cewa, "Wannan umarni ya tabbatar da cewa Sarki Aminu Ado Bayero yana da damar samun duk wani hakki da gata da matsayinsa ya samar masa.” A daya hannun kuma, Babbar Kotun Jihar Kano a karkashin mai shari’a Amina Adamu Aliyu, ta bayar da umarnin ba da kariya ga Muhammadu Sunusi da sauran manyan mutane daga duk wani cin zarafin da za a iya yi musu. "Wannan odar ta hana duk wata tsangwama ga ‘yancin cin gashin kan sarki da kuma ƙwace manyan alamomin ikonsa, kamar tagwayen masu da hular sarauta ta Dabo, da kuma takalman gashin jimina," kamar yadda umarnin ya ce.