Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Alhassan Yusuf ba zai buga wasan Nijeriya da Ivory Coast ba— Poseiro

An cire Yusuf ne a wasan Nijeriya da Equitorial Guinea bayan ya ji ciwo ranar Lahadi, kuma an tashi wasan 1-1. Kocin tawagar Nijeriya ta Super Eagles, Jose Poseiro ya tabbatar da cewar dan wasan tsakiya na kunfgiyar, Alhassan Yusuf ba zai buga wasan Nijeriya da Ivory Coast ba a Gasar Cin Kofin Af...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:07
Alhassan Yusuf ba zai buga wasan Nijeriya da Ivory Coast ba— Poseiro
A taƙaice

An cire Yusuf ne a wasan Nijeriya da Equitorial Guinea bayan ya ji ciwo ranar Lahadi, kuma an tashi wasan 1-1. Kocin tawagar Nijeriya ta Super Eagles, Jose Poseiro ya tabbatar da cewar dan wasan tsakiya na kunfgiyar, Alhassan Yusuf ba zai buga wasan Nijeriya da Ivory Coast ba a Gasar Cin Kofin Af...

An cire Yusuf ne a wasan Nijeriya da Equitorial Guinea bayan ya ji ciwo ranar Lahadi, kuma an tashi wasan 1-1. Kocin tawagar Nijeriya ta Super Eagles, Jose Poseiro ya tabbatar da cewar dan wasan tsakiya na kunfgiyar, Alhassan Yusuf ba zai buga wasan Nijeriya da Ivory Coast ba a Gasar Cin Kofin Afirka (AFCON) da ake yi a Ivory Coast. Kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN) ya ambato Poseiro ranar Laraba yana tabbatar da cewa sai a karawar da Nijeriya za ta yi da Guinea Bissau ne dan wasan zai buga wa Nijeriya. Alhassan Yusuf, wanda ke taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Royal Antwerp da ke Belgium, ya ji ciwo ne a wasan farko da Nijeriya ta buga da Equatorial Guinea a gasar AFCON. An cire Yusuf ne a wasan Nijeriya da Equitorial Guinea bayan ya ji ciwo ranar Lahadi, kuma an tashi wasan 1-1. Da yake magana da manema labarai a ranar Laraba, kocin na Nijeriya ya tabbatar da cewa Victor Osimhen zai buga wa Super Eagles a karawarsu da Eelephants na Ivory Coast.