Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Algeria 'ta juya da 'yan ci-rani kimanin 20,000 zuwa Jamhuriyar Nijar'

Tun shekarar 2014 'yan ci-rani, waɗanda suka haɗa da mata da yara, suna yawan bi ta Aljeriya a yunƙurin tsallaka Bahar Rum domin isa Turai amma hukumomi a Aljeriya suna juyawa da su. Aljeriya ta juya da 'yan ci-rani kusan 20,000 zuwa Jamhuriyar Nijar waɗanda suka taso daga ƙasashen yankin Sahara...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:07
Algeria 'ta juya da 'yan ci-rani kimanin 20,000 zuwa Jamhuriyar Nijar'
De un vistazo

Tun shekarar 2014 'yan ci-rani, waɗanda suka haɗa da mata da yara, suna yawan bi ta Aljeriya a yunƙurin tsallaka Bahar Rum domin isa Turai amma hukumomi a Aljeriya suna juyawa da su. Aljeriya ta juya da 'yan ci-rani kusan 20,000 zuwa Jamhuriyar Nijar waɗanda suka taso daga ƙasashen yankin Sahara...

Tun shekarar 2014 'yan ci-rani, waɗanda suka haɗa da mata da yara, suna yawan bi ta Aljeriya a yunƙurin tsallaka Bahar Rum domin isa Turai amma hukumomi a Aljeriya suna juyawa da su. Aljeriya ta juya da 'yan ci-rani kusan 20,000 zuwa Jamhuriyar Nijar waɗanda suka taso daga ƙasashen yankin Sahara zuwa Turai, kuma yawancinsu suna "cikin mummunan hali", a cewar wata ƙungiya mai zaman kanta da ke Yamai mai suna Alarme Phone Sahara a ranar Litinin. Tun shekarar 2014 'yan ci-rani, waɗanda suka haɗa da mata da yara, suna yawan bi ta Aljeriya a yunƙurin tsallaka Bahar Rum domin isa Turai amma hukumomi a Aljeriya suna juyawa da su. Ƙungiyar Alarme Phone Sahara -- wadda take ceto 'yan ci-rani daga saharar Aljeriya da Nijar -- ta ce an juya da 'yan ci-rani 19,798 zuwa Nijar daga watan Janairu zuwa Agusta, kamar yadda mai magana da yawunta Moctar Dan Yaye ya bayyana. Ana yawan barin 'yan ci-ranin cikin "mummunan yanayi" kuma akasari suna faɗawa yanayin "da ke iya kai wa ga mutuwarsu", a cewar ƙungiyar a rahoton da ta fitar a ƙarshen watan Agusta. "Ana kama 'yan ci-rani idan hukumomi suka kai samae a wuraren da suke fakewa ko inda suke aiki a birane, ko kuma a kan iyaka da Tunisiya sannan a ɗauke su zuwa Tamanrasset (kudancin Aljeriya) kafin a tuƙa su a manyan motocin a-kori-kura zuwa Nijar," in ji Yaye. Daga nan ne ake ɗaukar 'yan asalin Nijar a motoci zuwa Assamaka, wanda shi ne gari na farko na ƙasar Nijar da ke kan iyaka, inda ake miƙa su ga hukumomi. Su kuwa 'yan sauran ƙasashe, ana barinsu a wurin da ake kira "ihunka-banza", wani yankin sahara da ke kan iyakar Aljeriya da Nijar. Daga can, ana tilasta musu su yi tafiyar ƙafa ta kilomita 15 zuwa Assamaka a cikin matsanancin yanayi, a cewar Yaye. Yaye ya ƙara da cewa da zarar 'yan sandan Nijar da ke Assamaka sun kammala ɗaukar bayanan 'yan ci-ranin za su miƙa su ga cibiyoyin Majalisar Ɗinkin Duniya da Italiya inda ake tsugunar da su, kafin a tafi da su zuwa wasu cibiyoyin da ke arewacin Nijar. "Muna samun labarai da dama na cin zarafin da jami'an tsaron Aljeriya suke yi wa 'yan ci-rani da ƙwace kayayyakinsu," in ji shi. Hukumomin sojin Jamhuriyar Nijar sun yi sammacin jakadan Aljeriya a Nijar a watan Afrilu inda suka yi masa ƙorafi kan "mummunan yanayin" da 'yan ci-rani suke fuskanta a ƙasarsa kafin a juya da su zuwa Nijar. Sai dai hukumomin Aljeriya sun mayar da martani ta hanyar sammacin jakadan Nijar a ƙasarsu, sannan suka bayyana ƙorafin a matsayin "mara tushe".