Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 193 tana yi da Falasɗinawa da ke Gaza ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 33,797 da jikkata sama da mutum 76,465 a yayin da ƴan-kama-wuri-zauna da dakarun Isra'ila wajen kashe Falasɗinawa da ke Yammacin Kogin Jordan. 1616 GMT — Akwai yiwuwar ci gaba da fuskantar tashin hankali a Gabas ta Tsakiya har sai an daina da kisan ƙare dangi a Gaza — Erdogan Shugaba Erdogan na Turkiyya ya ce ana sa ran za a sake samun tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya har sai an kawo ƙarshen zalunci da kisan kare dangin da ake yi a Gaza. Erdogan ya kuma zargi Netanyahu na Isra'ila kan harin da Iran ta kai wa Isra'ilan yana mai cewa: "Babban wanda ke da alhakin tashin hankalin da ya dabaibaye zuƙatanmu a yammacin ranar 13 ga Afrilu shi ne Netanyahu da gwamnatinsa mai zubar da jini". Ya ƙara da cewa, Turkiyya ta ƙarfafa rawar da take takawa wajen samar da agajin jinƙai ga Gaza ta hanyar sake aikewa da jirgin ruwanta na 9 mai ɗauke da kayan agaji har tan 3,774. Shugaban na Turkiyya ya ƙara da cewa "Rikicinda ke ta'azzara, tana ci gaba da lalata gwamnatin Netanyahu da ba ta amfani kowa ba." Turkiyya ba ta yarda a sayar wa Isra'ila duk wani kayan da za a iya amfani da su don aikin soja ba tun kafin kisan kiyashin da ake yi a Gaza, in ji shi. 1257 GMT — Jordan ba za ta zama 'sansanin yaƙi tsakanin Isra'ila da Iran ba: Sarki Abdullah Lokacin da Iran ta kai hari kan Isra'ila a ƙarshen mako, Jordan ta daƙile makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa, amma Sarki Abdallah II ya jaddada cewa ba za a mayar da ƙasarsa "sansanin yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya ba". Sarki Abdallah II ya jaddada cewa ba za a mayar da ƙasarsa "sansanin yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya ba". / Photo: AA Idan yakin Gaza da ya ɓarke tun ranar 7 ga watan Oktoba ya haifar da kalubale masu tsauri ga kasar Jordan, yanzu tana fuskantar ƙarin barazanar maƙalewa a tsakiyar rikicin Isra'ila da Iran. Kasar Jordan wadda kusan rabin al’ummarta ‘yan asalin Falasdinu ne, ita ma aminiyar Amurka ce, ta kuma kulla yarjejeniyar zaman lafiya da maƙwabciyarta Isra’ila shekaru 30 da suka gabata. 1010 GMT — Adadin waɗanda suka mutu sakamakon yaƙin Isra'ila a Gaza ya kai 33,843 Aƙalla mutum 33,843 ne aka kashe a Gaza cikin sama da watanni shida da Isra’ila ta kwashe tana kai hare-hare, a cewar Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu a yankin da aka yi wa ƙawanya. Adadin waɗanda suka mutu ya hada da aƙalla mutum 46 da suka mutu a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, in ji sanarwar ma'aikatar, ta kuma ƙara da cewa mutum 76,575 ne suka jikkata a Gaza tun lokacin da aka fara yaƙin a ranar 7 ga watan Oktoba. 0640 GMT — Sojojin Isra'ila sun kai samame a wurare da dama a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan Sojojin Isra'ila sun kai samame a wurare da dama a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan inda suka kashe Falasɗinawa da dama, a cewar ganau. Dakarun Isra'ila sun kai samame a birnin Qalqilya da ke arewacin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, sannan sun kutsa kai cikin gidaje da dama a birnin, kamar yadda ganau suka tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu. Sun ƙara da cewa motocin sojojin Isra'ila sun riƙa buge motocin Falasɗinawa da gangan suna lalata su, yayin da kuma aka tura da sojojin Isra'ila gwanayen harbi daga ɓoye suka laɓe a rufin gidajen jama'a. Kazalika sojojin Isra'ila sun kai samame a garin Hableh da kudancin Qalqilya, inda suka kama aƙalla Falasɗinawa huɗu. Haka kuma an bayar da rahoton cewa dakarun Isra'ila sun kai samame a Tulkarem, Bethlehem, Ramallah, Hebron, da Jenin, inda suka tsare aƙalla Falasɗinawa biyar, a cewar ganau da suka gaya wa Anadolu. 0416 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa da dama a harin da ta kai ta sama a masallacin Jabalia na arewacin Gaza Jiragen yaƙin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa da dama sannan suka jikkata wasu a harin da suka kai da sanyin safiya a masallacin Jabalia da ke arewacin Gaza, a cewar kamfanin dillancin labaran Falasɗinawa WAFA. Majiyoyi daga asibiti sun ce “mutane da dama sun yi shahada sannan an kai mutum tara da suka jikkata Asibitin Kamal Adwan da ke arewacin Zirin Gaza sakamakon harin da jiragen yaƙin masu mamaya suka kai Masallacin Al Fakhourada ke sansanin ƴan gudun hijira na Jabalia.” Kazalika motocin sojojin Isra'ila sun shiga garin Beit Hanoun da ke arewacin Gaza, inda suka mamaye wata makaranta da mutane suke samun mafaka tare da buɗe musu wuta, in ji WAFA. Majiyoyi a yankin sun ce an katse duk wata sadarwa ciki har da ta intanet a yankin Beit Hanoun a yayin da dakarun Isra'ila suka yi kutse. 0005 GMT — Isra'ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa a Rafah Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla huɗu fararen-hula a yankin Tal al Sultan da ke Rafah, a yayin da ta kai sabon hari a sansanin Nuseirat da ke tsakiyar Gaza da kuma arewacin Gaza, kamar yadda ganau suka shaida wa TRT World. An kai wasu Falasɗinawa Asibitin Al Aqsa Martyrs sakamakon jikkatar da suka yi bayan harin da Isra'ila ta kai sansanin Nuseirat. / Hoto: AA 2200 GMT — Zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa ta ɓarke a wasu biranen Amurka Masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa sun toshe manyan hanyoyi a jihohin Illinois, California, New York da Oregon, lamarin da ya haddasa tarnaƙi ga masu zuwa Filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa na Chicago O'Hare, da gadojin Golden Gate and Brooklyn da ma hanyar West Coast mai cke da hada-hadar jama'a a yayin da Isra'ila ke ci gaba da mamaye Gaza. A Chicago, masu zanga-zanga sun toshe manyan hanyoyin da ke zuwa filayen jiragen sama da misalin ƙarfe bakwai na safe, a wani mataki da suka bayyana a matsayin "matsin lamba ta fuskar tattalin arziki domin ganin an bar Falasɗinawa sun sarara," a cewar Rifqa Falaneh, ɗaya daga cikin mutanen da suka jagorancin zanga-zangar. An katse tafiye-tafiye a birnin San Francisco na tsawon awanni a yayin da masu gangami suka toshe duk wasu manyan hanyoyin mota da na ƙafa da mahaya babura zuwa gadar Golden Gate Bridge inda suka kafa diram-diram cike da ƙasa da siminti suka toshe babbar hanyar Interstate 880 da ke Oakland. Masu zanga-zanga da suka yi tattaki a Brooklyn sun toshe hanyar da ke isa Manhattan daga kan Gadar Brooklyn. A yankin Eugene na Oregon, masu zanga-zanga sun toshe hanyar Interstate 5, inda suka kawo tsaiko a tafiye-tafiye na fiye da minti 45. An tura gomman ƴan sanda wurin da masu zanga-zanga suke yayin da suka toshe Gadar Golden Gate Bridge da ke San Francisco./Hoto:AA
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Akwai yiwuwar ci gaba da fuskantar tashin hankali a Gabas ta Tsakiya har sai an daina da kisan ƙare dangi a Gaza — Erdogan
Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 193 tana yi da Falasɗinawa da ke Gaza ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 33,797 da jikkata sama da mutum 76,465 a yayin da ƴan-kama-wuri-zauna da dakarun Isra'ila wajen kashe Falasɗinawa da ke Yammacin Kogin Jordan. 1616 GMT — Akwai yiwuwar ci gaba da fuskantar t...

At a glance
Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 193 tana yi da Falasɗinawa da ke Gaza ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 33,797 da jikkata sama da mutum 76,465 a yayin da ƴan-kama-wuri-zauna da dakarun Isra'ila wajen kashe Falasɗinawa da ke Yammacin Kogin Jordan. 1616 GMT — Akwai yiwuwar ci gaba da fuskantar t...
