الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Akalla mutum 73 sun rasu a Iran bayan 'fashewar bam' kusa da kabarin Qasem Soleimani

Dumbin mutane ne suka taru a ranar Laraba domin tunawa da kisan da Amurka ta yi wa Janar Qasem Soleimani wanda kafin mutuwarsa kwamanda ne a rundunar juyin juya hali ta Iran. Akalla mutum 73 aka kashe a Iran bayan wasu abubuwa sun fashe sau biyu a cikin taron wasu mutane wadanda suke tunawa da ki...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:07 ص
Akalla mutum 73 sun rasu a Iran bayan 'fashewar bam' kusa da kabarin Qasem Soleimani
لمحة سريعة

Dumbin mutane ne suka taru a ranar Laraba domin tunawa da kisan da Amurka ta yi wa Janar Qasem Soleimani wanda kafin mutuwarsa kwamanda ne a rundunar juyin juya hali ta Iran. Akalla mutum 73 aka kashe a Iran bayan wasu abubuwa sun fashe sau biyu a cikin taron wasu mutane wadanda suke tunawa da ki...

Dumbin mutane ne suka taru a ranar Laraba domin tunawa da kisan da Amurka ta yi wa Janar Qasem Soleimani wanda kafin mutuwarsa kwamanda ne a rundunar juyin juya hali ta Iran. Akalla mutum 73 aka kashe a Iran bayan wasu abubuwa sun fashe sau biyu a cikin taron wasu mutane wadanda suke tunawa da kisan Janar Qasem Soleimani wanda aka kashe a 2020. “Akalla mutum 73 suka rasa rayukansu a wannan lamari” wanda ya faru a ranar Laraba a kusa da kabarin shugaban dakarun juyin juya hali na Iran a wani masallaci da ke kudancin birnin Kerman, kamar yadda gidan talabijin na kasar ya ruwaito. Kafar watsa labarai ta Nournews ta ce “tukwanen gas da dama sun fashe a hanyar zuwa makabartar”. An ruwaito jami’in kasar yana cewa “babu tabbaci kan ko tukwanen gas ne ko harin ta’addanci ne”. Kafar watsa labarai ta ta nuna masu ceto na kungiyar bayar da agaji ta Red Crescent suna taimaka wa wadanda suka samu raunin. Wasu kafafen watsa labarai na Iran din a nasu bangaren sun ruwaito cewa mutum 50 sun rasu sakamakon tashin bam din. “Kungiyoyinmu na kai agajin gaggawa suna kwashe wadanda suka ji rauni... Sai dai akwai dumbin mutane wadanda suka toshe hanya,” in ji Reza Fallah, shugaban kungiyar Red Crescent reshen lardin Kerman.