Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Afirka ta Kudu na cikin shirin ko-ta-kwana game da ambaliyar ruwa

Hukumomi sun ce mahaukaciyar iska ta yi ta'adi a ƙarshen mako, inda ta ɓaɓɓake rufin gidaje ta kuma kayar da bishiyu a yankin Western Cape. Afirka ta Kudu ta sanar da shiga shirin ko-ta-kwana na Kwamitin Magance Bala'i a Western Cape, bayan da aka yi gargaɗin yiwuwar faruwa mummunar ambaliya a ya...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:07
Afirka ta Kudu na cikin shirin ko-ta-kwana game da ambaliyar ruwa
A taƙaice

Hukumomi sun ce mahaukaciyar iska ta yi ta'adi a ƙarshen mako, inda ta ɓaɓɓake rufin gidaje ta kuma kayar da bishiyu a yankin Western Cape. Afirka ta Kudu ta sanar da shiga shirin ko-ta-kwana na Kwamitin Magance Bala'i a Western Cape, bayan da aka yi gargaɗin yiwuwar faruwa mummunar ambaliya a ya...

Hukumomi sun ce mahaukaciyar iska ta yi ta'adi a ƙarshen mako, inda ta ɓaɓɓake rufin gidaje ta kuma kayar da bishiyu a yankin Western Cape. Afirka ta Kudu ta sanar da shiga shirin ko-ta-kwana na Kwamitin Magance Bala'i a Western Cape, bayan da aka yi gargaɗin yiwuwar faruwa mummunar ambaliya a yankin ranar Litinin. Cibiyar kula da yanayi ta Afirka ta Kudu ta fitar da gargaɗin mataki na tara, kan yiwuwar ambaliya, inda hakan ya sanya hukumomi suka rufe makarantu ranar Litinin. SCHOOL CLOSURE ALERT ???? Please follow official accounts for accurate information. https://t.co/hcBNZeTw0J — Western Cape Gov (@WesternCapeGov) April 7, 2024 An saka jami'an agaji cikin shiri, kuma hukumomi sun ce, iska mai ƙarfi ta yi ta'adi a faɗin yankin cikin ƙarshen mako, kuma ta ɓaɓɓake rufin gidaje da kayar da bishiyu. Yawancin tituna da gidajen Gundumar Moqhaka, sun faɗa cikin ambaliyar, sakamakon mamakon ruwan sama da ya shafi unguwannin Kroonstad da Maokeng, cewar rahotanni daga SABC na Afirka ta Kudu. Certain areas in the Western Cape are at high risk of floods due to the predicted intense downpours. Do not cross rivers and stay away from open bodies of water that may pose a risk to your health and life. Take the necessary precautions, be vigilant and keep safe! pic.twitter.com/7WoAauiCiM — Western Cape Gov (@WesternCapeGov) April 7, 2024 Kakakin unguwar Dika Kheswa ya faɗa wa 'yan jarida a yankin cewa gundumar ba za ta iya tantance yawan ta'adin ba a yanzu. An shawarci mazauna yankin su guje wa wuraren da ke kwari da kuma gadoji. Hukumomin sun ƙara da cewa ƙaƙƙarfar iska ce ta haddasa gobara kusan 40 a yankin, cikinsu har da gobarar da ta lamushe kusan bukkoki 300, kuma ta shafi kusan mutane 2,000 zuwa yanzu.