Idan Osimhen bai buga wasan ba, hakan zai zama cikas ga tawagar Super Eagles da ta kai matakin wasan kusa da na karshe bayan doke kasar Angola da ci 1-0. Watakila shahararren dan wasan Nijeriya Victor Osimhen bai zai buga wasan matakin kusa da na karshe ba da kasarsa za ta yi da Afirka ta Kudu a birnin Bouake na kasar Ivory Coast ranar Laraba, in ji tawagar Nijeriya. Dan wasan gaban Napoli ba ya cikin ’yan wasan da suka yi tafiya a ranar Litinin zuwa birnin Bouake saboda ciwon cikin da yake damunsa, kamar yadda mai magana da yawun tawagar Super Eagles Babafemi Raji ya bayyana. “Masu kula da lafiyar ’yan wasa sun tabbatar da cewa dan wasan yana karkashin kulawarsu a birnin Abidjan,” in ji shi. Ya ci gaba da cewa ’’idan an sallame shi zuwa gobe (Talata) da safe, zai hadu da sauran ’yan wasan.” Gasa mai cike da kalubale Osimhen wanda shi ne Gwarzon Dan Kwallon Kafar Afirka bai yi atisaye ba ranar Litinin gabanin lokacin da tawagar ta kama hanyar barin birnin Abidjan. An canja Osimhen yayin wasan gab da na kusa da na karshe da Angola ana kusa da tashi wasan a karshen mako. Dan kwallon mai shekara 25 ya ci kwallo daya kuma ya taimaka an ci wata kwallon a gasar. Bayan Nijeriya ta kai matakin wasan kusa da na karshe, Kocin Super Eagles Jose Peseiro ya ce “Ina farin ciki tare da ’yan wasana. Sun cancanci samun wannan nasara.” “Sun mana komai, ga Super Eagles ga mutum miliyan 220. Sun yi aiki sosai, sun yi aiki sosai, sun yi aiki sosai. Wannan gasa ba ta da sauki.”
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
AFCON 2023: Watakila Victor Osimhen ba zai buga wasan Nijeriya da Afirka ta Kudu ba
Idan Osimhen bai buga wasan ba, hakan zai zama cikas ga tawagar Super Eagles da ta kai matakin wasan kusa da na karshe bayan doke kasar Angola da ci 1-0. Watakila shahararren dan wasan Nijeriya Victor Osimhen bai zai buga wasan matakin kusa da na karshe ba da kasarsa za ta yi da Afirka ta Kudu a...

At a glance
Idan Osimhen bai buga wasan ba, hakan zai zama cikas ga tawagar Super Eagles da ta kai matakin wasan kusa da na karshe bayan doke kasar Angola da ci 1-0. Watakila shahararren dan wasan Nijeriya Victor Osimhen bai zai buga wasan matakin kusa da na karshe ba da kasarsa za ta yi da Afirka ta Kudu a...
