Главная / Архив новостей
Архив новостей

В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.

Adadin wadanda suka mutu a Gaza sakamakon yakin Isra'ila ya kai 19,400

Yakin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza - ya kwana na 73 - inda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 18,800, da jikkata wasu fiye da 51,000, yayin da ake fargabar dubban mutane sun mutu a karkashin baraguzan gine-ginen da aka kai wa hari. 1331 GMT — Harin Isra'ila ya shafi a asibitin Shifa na Ga...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Обновлено 13.08.2026, 05:26:07
Adadin wadanda suka mutu a Gaza sakamakon yakin Isra'ila ya kai 19,400
Кратко

Yakin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza - ya kwana na 73 - inda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 18,800, da jikkata wasu fiye da 51,000, yayin da ake fargabar dubban mutane sun mutu a karkashin baraguzan gine-ginen da aka kai wa hari. 1331 GMT — Harin Isra'ila ya shafi a asibitin Shifa na Ga...

Yakin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza - ya kwana na 73 - inda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 18,800, da jikkata wasu fiye da 51,000, yayin da ake fargabar dubban mutane sun mutu a karkashin baraguzan gine-ginen da aka kai wa hari. 1331 GMT — Harin Isra'ila ya shafi a asibitin Shifa na Gaza: shaidu Wani hari ta sama da Isra'ila ta kai ya fada kan a asibiti mafi girma na Gaza, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, kamar yadda shaidu suka bayyana. Tashar talabijin ta Aljazeera ta watsa wani bidiyo da ke nuna sakamakon harin da aka kai a asibitin Shifa da ke birnin Gaza, inda ake iya ganin gawarwaki birjik a kasa a cikin harabar asibitin, wanda ya unshi gine-gine da dama. Wasu mutum biyu da ke samun mafaka a asibitin sun tabbatar da faruwar harin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press. 1406 GMT — A dadin wadanda suka mutu a Gaza sakamakon hare-haren Isra'ila ya kai 19,400 — jami'ai Ma'aikatar Lafiya a Gaza da aka yi wa ƙawanya ta ce akalla mutum 19,453 ne suka mutu a yankin Falasdinawa sakamakon mummunan yaƙin da Isra'ila ke yi tun ranar 7 ga watan Oktoba. A cewar ma'aikatar, mutum 52,286 ne suka samu raunuka a Gaza a tsawon sama da watanni biyu da aka shafe ana gwabzawa. 1129 GMT — Shugaban CIA zai gana da jami'an Isra'ila da Qatari kan batun fursunoni Daraktan hukumar leken asiri ta Amurka CIA zai gana da Firaministan Qatar Mohammed bin Abdulrahman Al Thani da shugaban hukumar leƙen asirin Isra'ila Mossad a birnin Warsaw, don tattauna wata sabuwar yarjejeniya don ganin an saki Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su a Gaza, kamar yadda shafin Axios ya rawaito, yana ambato wasu jami'an Amurka da Isra'ila biyu. 1247 GMT — Ana zargin sojojin Isra’ila da cunawa wa marasa lafiya karnuka Sojojin Isra'ila na amfani da karnuka wurin kai hare-hare ga Falasdinawa. / Hoto: Reuters Hukumomi a Gaza sun yi kira kan a gudanar da bincike bayan an zargi sojojin Isra’ila da amfani da buldoza wurin rusa gidaje da kuma cunna wa marasa lafiya karnuka a asibitin Kamal Adwan. Sojojin na Isra’ila sun kai samame asibitin Kamal Adwan a makon da ya gabata da kuma yi masa ruwan harsasai na tsawon kwanaki. Hukumomin sun ce marasa lafiyan da aka cinuwa karnukan suna dauke da raunuka a jikinsu. 0820 GMT — Isra'ila ta ce an kara kashe sojojinta hudu a Gaza Sojojin Isra’ila a ranar Litinin sun ce an kara kashe jami’ansu hudu an raunata daya a yakin da suke yi da Falasdinawa a kudancin Gaza, wanda hakan ya sa adadin sojojin na Isra’ila da aka kashe ya kai 458. Sojojin na Isra’ila na ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza tun bayan da Hamas ta kai hari watanni biyu da suka gabata, inda suka kashe Falasdinawa 18,800 da kuma raunata 51,000 wadanda akasarinsu yara ne da mata. Haka kuma sojojin sun lalata dubban gine-gine da ababen more rayuwa na Falasdinawan a yakin da suke ci gaba da yi. 0732 GMT — Isra'ila ta kashe 'yan gudun hijira 90 a wani sansani da ke Gaza Isra’ila ta kaddamar da munanan hare-hare a Gaza, inda ta kai hari a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke arewacin birnin, da kuma asibiti a kudanci inda sojojin suka kashe wata matashiya wadda ta rasa kafarta a wani hari na baya da suka kai, kamar yadda hukumomin Falasdinu suka shaida. Harin da Isra’ila ta kai sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 90, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar lafiya ta Gaza ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters. Wani makami mai linzami da aka harba a gidan iyalan Shehab ya yi sanadin mutuwar mutum 24, kamar yadda gidan rediyon Aqsa na Hamas ya sanar. Hare-haren Isra'ila na ci gaba da kashe kananan yara da mata a Gaza. / Hoto: Reuters 0000 GMT — WHO ta yi tur da 'lalata' asibitin Kamal Adwan na Gaza Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya ya yi Allah wadai da "mummunar ɓarnar" da aka yi a asibitin Kamal Adwan da ke arewacin Gaza, inda ya kara da cewa akalla majiyyata takwas ne suka mutu. Daga cikin majinyatan da suka rasu har da wani yaro dan shekara tara, in ji Tedros Adhanom Ghebreyesus a wani sako da ya wallafa a shafin X. Bayanin nasa ya zo ne a daidai lokacin da sojojin Isra'ila suka fice daga asibitin bayan wani samame da suka shafe kwanaki suna yi, suna masu cewa kungiyar Hamas ta yi amfani da shi a matsayin cibiyar bayar da umarni. Hamas dai ta sha musanta irin wannan ikirarin. Tedros ya rubuta "@WHO ta yi matukar mamakin yadda aka lalata asibitin Kamal Adwan da ke arewacin #Gaza a cikin 'yan kwanakin da suka gabata, lamarin da ya sa ba ya aiki kuma hakan ya jawo sanadin mutuwar aƙalla mutum takwas." Ya kara da cewa, "An ce an tsare ma'aikatan lafiya da dama, kuma WHO da abokan huldarsu na neman bayanai cikin gaggawa kan halin da suke ciki." 0130 GMT — Hukumomin Falasdinu sun bukaci Faransa da ta taimaka wajen warware rikicin 'yan kama wuri zauna a Gabar Yammacin Kogin Jordan Hukumomin Falasdinu sun bukaci Faransa da ta taimaka wajen warware hare-haren da 'yan kama wuri zauna ke kai wa Falasdinawa a Gabar Yammacin Kogin Jordan. A yayin ganawar da Firaministan Falasdinu Muhammad Shtayyeh da takwararsa ta Harkokin Wajen Faransa Catherine Colonna suka yi a birnin Ramallah da ke Yammacin Gabar Kogin Jordan, Shtayyeh ya jaddada wajabcin matsa wa Isra'ila lamba kan ta daina cin zarafin Falasdinawa a yankin Yammacin Gabar Kogin Jordan da ta mamaye, ciki har da Gabashin Birnin Ƙudus. Shtayyeh ya kuma yi kira da a bude dukkan mashigan Zirin Gaza domin ba da damar shigar da kayan agaji da magunguna da man fetur da kuma dawo da ayyukan wutar lantarki da na ruwa. Har ila yau, ya jaddada muhimmancin goyon bayan Faransa don amincewa da kasar Falasdinu tare da zama cikakiyar mamba a Majalisar Dinkin Duniya. 0020 GMT - Ana yi wa Isra'ila sabbin kiraye-kirayen tsagaita wuta bayan da kisan mutanen da aka yi garkuwa da su ya haifar da fargaba kan ayyukanta a Gaza Gwamnatin Isra'ila ta fuskanci kiraye-kirayen cimma sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta daga wasu makusantanta na Turai, bayan wasu jerin harbe-harbe da suka hada da kisan da aka yi wa wasu Isra'ilawa uku da aka yi garkuwa da su cikin "kuskure", lamarin da ya kara tayar da hankalin duniya game da yakin da aka kwashe makonni 10 ana yi a Gaza. Masu zanga-zangar a Isra'ila suna kira ga gwamnatinsu da ta sabunta tattaunawa da gwamnatin Hamas ta Gaza, wadda Isra'ila ta sha alwashin rusawa. Ana kuma sa ran Isra'ila za ta fuskanci matsin lamba don rage manyan ayyukan yaki a lokacin da sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin zai kai ziyara a yau Litinin