Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Adadin mutanen da suka mutu bayan wani mutum ya kutsa babbar mota cikin taron jama'a a New Orleans na Amurka sun kai 15

Jami'in da ke gudanar da bincike kan abin da ya haddasa mutuwar jama'a a birnin New Orleans Coroner ya ce za a kwashe wasu kwanaki kafin samun sakamakon gwaji don gano mutanen da suka mutu. Adadin mutanen da suka mutu bayan wani mutum ya kutsa wata babbar motar daukar kaya cikin taron jama'a a bi...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:07
Adadin mutanen da suka mutu bayan wani mutum ya kutsa babbar mota cikin taron jama'a a New Orleans na Amurka sun kai 15
En bref

Jami'in da ke gudanar da bincike kan abin da ya haddasa mutuwar jama'a a birnin New Orleans Coroner ya ce za a kwashe wasu kwanaki kafin samun sakamakon gwaji don gano mutanen da suka mutu. Adadin mutanen da suka mutu bayan wani mutum ya kutsa wata babbar motar daukar kaya cikin taron jama'a a bi...

Jami'in da ke gudanar da bincike kan abin da ya haddasa mutuwar jama'a a birnin New Orleans Coroner ya ce za a kwashe wasu kwanaki kafin samun sakamakon gwaji don gano mutanen da suka mutu. Adadin mutanen da suka mutu bayan wani mutum ya kutsa wata babbar motar daukar kaya cikin taron jama'a a birnin New Orleans na jihar Louisiana a Amurka ya karu zuwa 15, a cewar jami'in da ke bincike kan sanadin mutuwa na New Orleans Dr Dwight McKenna. "A halin da ake cikin mutum 15 ne suka mutu. Za a kwashe kwanaki da dama kafin gudanar da gwaje-gwaje kan gawawwakin dukkan mutanen. Da zarar an kammala gwaje-gwajen kuma mun tattauna da 'yan'uwan mutanen, za mu fitar da sunayensu,"in ji McKenna a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba. Tun da fari, an tabbatar da jikkatar mutum 35 bayan mutumin da ke cikin babbar motar daukar kaya ya kutsa cikin dandazon jama'a a unguwar French Quarter da misalin karfe 3.15 na safe (0915GMT) ranar Laraba. Unguwar ta shahara saboda yadda masu yawon bude ido suke zuwa yankin domin gudanar da bukukuwan sabuwar shekara, musamman a jajiberen Sabuwar Shekara. 'Yan sanda sun ce mutumun ya tuka motar ta gefen hanya kusa da wurin da jami'an 'yan sanda suka ajiye motarsu inda ya mamayi jama'a ya kutsa cikinsu.