Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a Gaza ya kai 40,476 a yayin da take ci gaba da luguden wuta

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 326, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,435— galibinsu mata da yara — tare da jikkata fiye da mutum 93,534, sannan an yi amanna cewa ɓaraguzan gine-gine sun danne fiye da mutum 10,000. Talata, 27 ga watan Agusta, 2024 0821 GMT — Adadin mutanen...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:07
Adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a Gaza ya kai 40,476 a yayin da take ci gaba da luguden wuta
De un vistazo

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 326, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,435— galibinsu mata da yara — tare da jikkata fiye da mutum 93,534, sannan an yi amanna cewa ɓaraguzan gine-gine sun danne fiye da mutum 10,000. Talata, 27 ga watan Agusta, 2024 0821 GMT — Adadin mutanen...

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 326, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,435— galibinsu mata da yara — tare da jikkata fiye da mutum 93,534, sannan an yi amanna cewa ɓaraguzan gine-gine sun danne fiye da mutum 10,000. Talata, 27 ga watan Agusta, 2024 0821 GMT — Adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a Gaza ya kai 40,476 a yayin da take ci gaba da luguden wuta Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla 40,476 a yaƙin kisan ƙare-dangi da ta kwashe watanni 11 tana yi a Gaza, a cewar Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta yankin. Adadin ya haɗa da mutum 41 da jiragen yaƙinta suka kashe a awa 24 da suka wuce, a cewar sanarwar da ma'aikatar ta fitar. Ta ƙara da cewa Isra'ila ta jikkata mutum 93,647 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba da ta ƙaddamar da yaƙi a yankin. 2020 GMT —Sojojin Isra'ila da Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna sun kashe Falasɗinawa Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla shida a Birnin Gaza na yankin Falasɗinu bayan jiragen yaƙinta sun kai hari wani gida. Jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hari a sansanin 'yan gudun hijira na Maghazi, inda suka kashe Falasɗinawa aƙalla uku, ciki har da jariri, tare da jikkata wasu, a cewar kamfanin dillancin labaran Falasɗinu WAFA. Ya ƙara da cewa jami'an hukumar bayar da agajin gaggawa sun gano gawa uku tare da mutanen da suka jikkata bayan Isra'ila ta yi luguden wuta a wani gida na iyalan Na'san a Layin Yermouk na Birnin Gaza. Falasɗinawa suna jimamin kisan da Isra'ila ta yi wa 'yan'uwansu a lardin Al Mawasi, cikinsu har da wani ɗan ƙungiyar 'yan jarida, Ali Taima, a Asibitin Nasser a Khan Younis / Hoto: AA 2128 GMT — 'Yan kama-wuri-zauna sun kashe Bafalasɗine a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan 'Yan kama-wuri-zauna sun kashe wani Bafalasɗine tare da jikkata wasu uku a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, in ji Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Falasɗinu — a hare-hare fiye da 1,270 da 'yan ta'adda masu tsananin kishin kafa ƙasar Isra'ila suka ƙaddamar a kan Falasɗinawa tun watan Oktoban da ya gabata. Sojojin Isra'ila da da Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna sun kashe Falasɗinawa aƙalla 680 sannan suka jikkata kusan 6,000 a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan. Amurka da wasu ƙasashen Tarayyar Turai sun sanya takunkumai kan 'yan kama-wuri-zauna masu tayar da hanklai sannan sun sha yin kira ga Isra'ila ta hana su kai hare-hare kan Falasɗinawa. Sai dai hakan bai hana 'yan kama-wuri-zauna da masu kare su ci gaba da kashe Falasɗinawa ba. Gwamnatin Isra'ila cike take da shugabannin Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna da kuma masu tsananin kishin kafa ƙasar Isra'ila, waɗanda suka kafa rundunar mayaƙan sa-kai a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da Gabashin Birnin Ƙudus.