Hadaddiyar Daular Larabawa ce ke karbar bakuncin taron sauyin yanayi na wannan shekarar, kuma tana da mahalarta mafi yawa -- wato mutum 4,409, Brazil na da mahalarta 3,081 sai Nijeriya da China da kowaccensu ke da mahalarta 1,411. Ce-ce-ku-ce ya mamaye taron COP28 na sauyin yanayi da ake yi a Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa yayin da ‘yan Nijeriya ke korafi kan dumbin ‘yan kasar da suka halarci taron. Taron na sauyin yanayi taro ne na shekara-shekara wanda a bana Hadaddiyar Daular Larabawa ce ke da mahalarta taron mafi yawa inda take da mutum 4,409 sai Brazil mutum 3,081 sai Nijeriya da China masu 1,411. Wannan dalili ne ya sa ‘yan Nijeriyar da dama musamman a shafukan sada zumunta suka fito suna korafi kan cewa bai kamata gwamnatin Nijeriyar ta dauki nauyin dumbin mutanen nan ba a daidai lokacin da kasar ke fama da matsaloli na matsin tattalin arziki. Sai dai a sanarwar da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa ba ita ta dauki nauyin mutum 1,411 da ke halartar taron ba, inda ta ce akwai mutane da dama da kamfanoni wadanda ba ita ta dauki nauyinsu ba. Korafin wasu ‘yan Nijeriya In a twist of sad irony, let me congratulate the giant of Africa, Nigeria, for matching the great China, with the same number of contingents at the ongoing COP28 in Dubai, United Arab Emirates. Nigeria's contingent to COP28 totaled 1411, the same number as the Chinese — Peter Obi (@PeterObi) December 3, 2023 Daga cikin masu yin wannan korafin, har da dan takarar shugabancin Nijeriya a Jam’iyyar Labour Peter Obi wanda ya yi wa kasar shagube tare da caccakar kasar a kaikace kan wannan mataki. December 3, 2023 Press Statement PDP Queries Tinubu’s Over-bloated COP28 Delegation …Asks FG To Come Clean on Government Roll Call, Cost The Peoples Democratic Party (PDP) @OfficialPDPNig queries President Bola Ahmed Tinubu @officialABAT over his over-bloated delegation of… pic.twitter.com/jtlU5Bv1Fp — Official PDP Nigeria (@OfficialPDPNig) December 3, 2023 Ita ma sanarwar da mai magana da yawun Jam’iyyar PDP Debo Ologunagba ya fitar ta yi Allah wadai da wannan lamari inda ta ce asarar kudin kasa ne. Jam’iyyar ta ce bai kamata gwamnatin Nijeriyar ta kashe irin wadannan kudaden ba a daidai lokacin da kasar ke fuskantar kalubale na tattalin arziki. Me gwamnatin Nijeriya ke cewa? A wata sanarwa da Ma’aikatar Watsa Labarai ta Nijeriya ta fitar a ranar Lahadi, ta tabbatar da cewa akwai ‘yan kasar da dama da ba Nijeriya ta dauki nauyinsu ba. Nigeria at COP28: Separating The Facts From Fiction By Temitope Ajayi The number of delegates from Nigeria attending the ongoing Climate Summit in Dubai otherwise called COP28 has generated a lot of controversies and strong social media conversations in the last 24 hours. It… — Fed Min of Info & Nat’l Orien (@FMINONigeria) December 3, 2023 Gwamnatin Nijeriyar ta ce daga cikin wadanda suka halarci taron daga kasar akwai shugaban bankin UBA Tony Elumelu da Abdul Samad Rabiu Shugaban BUA da sauran masu kudi ‘yan kasuwa. Gwamnatin Nijeriyar ta jaddada cewa wadannan ‘yan kasuwan sun taho da ma’aikatansu domin ci gaban kasuwancinsu, kuma suna daga cikin mutum 1,411 daga Nijeriya inda ta ce ba gwamnatin tarayya ce ta dauki nauyinsu ba. It is honorable to clarify that not all Nigerian delegates attending #COP28 in Dubai are sponsored by the federal government. As a duly nominated delegate myself, I can attest that many individuals, including myself, are representing Nigeria independently. Our involvement is not… pic.twitter.com/GH4qyy3fbV — Bashir Ahmad (@BashirAhmaad) December 3, 2023 Daya daga cikin hadiman tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari wato Bashir Ahmed ya tabbatar da batun na gwamnatin Nijeriyar inda ya wallafa takardar gayyatar da aka yi masa tare da cewa shi ya dauki nauyin kansa.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Abin da ya sa zuwan 'yan Nijeriya 1,411 taron COP28 a Dubai ya jawo ce-ce-ku-ce
Hadaddiyar Daular Larabawa ce ke karbar bakuncin taron sauyin yanayi na wannan shekarar, kuma tana da mahalarta mafi yawa -- wato mutum 4,409, Brazil na da mahalarta 3,081 sai Nijeriya da China da kowaccensu ke da mahalarta 1,411. Ce-ce-ku-ce ya mamaye taron COP28 na sauyin yanayi da ake yi a Dub...

At a glance
Hadaddiyar Daular Larabawa ce ke karbar bakuncin taron sauyin yanayi na wannan shekarar, kuma tana da mahalarta mafi yawa -- wato mutum 4,409, Brazil na da mahalarta 3,081 sai Nijeriya da China da kowaccensu ke da mahalarta 1,411. Ce-ce-ku-ce ya mamaye taron COP28 na sauyin yanayi da ake yi a Dub...
