Главная / Архив новостей
Архив новостей

В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.

Aƙalla mutum takwas sun rasu, 15 sun ɓace sakamakon ambaliyar ruwa a Morocco

A ranar Juma'a babban daraktan kula da yanayi na kasar Maroko ya yi gargadi game da ruwan sama mai tsawon milimita 150 a yankuna da dama na kasar da ke arewacin Afirka. Akalla mutane takwas ne suka mutu yayin da wasu 15 suka ɓace sakamakon ambaliyar ruwa a kudu maso gabashin Maroko, kamar yadda h...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Обновлено 13.08.2026, 05:26:07
Aƙalla mutum takwas sun rasu, 15 sun ɓace sakamakon ambaliyar ruwa a Morocco
Кратко

A ranar Juma'a babban daraktan kula da yanayi na kasar Maroko ya yi gargadi game da ruwan sama mai tsawon milimita 150 a yankuna da dama na kasar da ke arewacin Afirka. Akalla mutane takwas ne suka mutu yayin da wasu 15 suka ɓace sakamakon ambaliyar ruwa a kudu maso gabashin Maroko, kamar yadda h...

A ranar Juma'a babban daraktan kula da yanayi na kasar Maroko ya yi gargadi game da ruwan sama mai tsawon milimita 150 a yankuna da dama na kasar da ke arewacin Afirka. Akalla mutane takwas ne suka mutu yayin da wasu 15 suka ɓace sakamakon ambaliyar ruwa a kudu maso gabashin Maroko, kamar yadda hukumomi suka sanar a ranar Lahadi. "An gano gawarwakin mutum takwas, yayin da wasu 15 suka ɓace a ambaliyar da ta yi sanadin rugujewar gidaje da dama a birnin Tata," in ji Omar Bahoush, magajin yankin Tamanart, a tattaunawarsa da gidan talabijin na Channel 2 na yankin. Ambaliyar ruwan wadda ta afku da yammacin ranar Asabar, ta yi barna sosai a yankin, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka bayyana. A ranar Juma'a babban daraktan kula da yanayi na kasar Maroko ya yi gargadi game da ruwan sama mai tsawon milimita 150 a yankuna da dama na kasar da ke arewacin Afirka. Ambaliyar ruwa Bahoush ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa ambaliyar ta lmamaye tituna tare da lalata hanyoyin sadarwa a birnin, wanda hakan ya kawo cikas wurin gano ainahin adadin mutanen da suka ɓace. Kudancin Maroko dai ya jima yana fuskantar ruwan sama kamar da bakin kwarya a cikin 'yan kwanakin nan, wanda ya sake cika madatsun ruwa na ƙasar waɗanda suka jima suna fuskantar ƙarancin ruwan sakamakon raguwar da aka samu na ruwa a 'yan shekarun nan. Sai dai wannan ruwan ya jawo barazana matuƙa ga ɓangaren noma na ƙasar. Ko a ranar Laraba sai da mutum uku suka rasu sakamakon ambaliyar da ta shafe wasu birane a gabashin Maroko sakamakon mamakon ruwan sama.