Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Aƙalla mutum 20 sun mutu bayan da kwale-kwalensu ya kama da wuta a Bayelsan Nijeriya

Kwale-kwalen na ɗauke ne da 'yan kasuwar da ke kai kaya yankunan da ke gaɓar teku, a cewar mai magana da yawun undunar 'yan sanda Nijeriya ta jihar Bayelsa, Musa Muhammed a ranar Alhamis. Aƙalla mutum 20 ne suka mutu sakamakon kama wuta tare da fashewa da wani kwale-kwalen katako da suke ciki ya...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:07
Aƙalla mutum 20 sun mutu bayan da kwale-kwalensu ya kama da wuta a Bayelsan Nijeriya
En bref

Kwale-kwalen na ɗauke ne da 'yan kasuwar da ke kai kaya yankunan da ke gaɓar teku, a cewar mai magana da yawun undunar 'yan sanda Nijeriya ta jihar Bayelsa, Musa Muhammed a ranar Alhamis. Aƙalla mutum 20 ne suka mutu sakamakon kama wuta tare da fashewa da wani kwale-kwalen katako da suke ciki ya...

Kwale-kwalen na ɗauke ne da 'yan kasuwar da ke kai kaya yankunan da ke gaɓar teku, a cewar mai magana da yawun undunar 'yan sanda Nijeriya ta jihar Bayelsa, Musa Muhammed a ranar Alhamis. Aƙalla mutum 20 ne suka mutu sakamakon kama wuta tare da fashewa da wani kwale-kwalen katako da suke ciki ya yi a jihar Bayelsa da ke kudu maso kudancin ƙasar a ranar Laraba, in ji 'yan sanda Kwale-kwalen na ɗauke ne da 'yan kasuwar da ke kai kaya yankunan da ke gaɓar teku, a cewar mai magana da yawun undunar 'yan sanda Nijeriya ta jihar Bayelsa, Musa Muhammed a ranar Alhamis. 'Yan kasuwa kan je yankunan da ke gaɓar teku da kuma babban birnin jihar Yenagoa a duk mako. Aƙalla mutum 200 ne rahotanni suka ce sun mutu sakamakon hatsarin kwale-kwale a Nijeriya a bara kawai, inda hukumomi ke cewa ana yawan samun hakan ne saboda lodi mai yawa da rashin kula da jiragen ruwan.