Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

A shirye Turkiyya take ta karɓi baƙuncin COP31, da taimakawa don sake gina Gaza: Erdogan

Turkiyya ce za ta shirya taron COP31 na shekara mai zuwa a garin shakatawa na bakin teku na Antalya, bayan da Australia ta janye neman ta na ɗaukar nauyin wannan taro na shekara-shekara. Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce Turkiyya ta shirya karɓar baƙuncin taron Majalisar Ɗinkin D...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:07
A shirye Turkiyya take ta karɓi baƙuncin COP31, da taimakawa don sake gina Gaza: Erdogan
Kwa muhtasari

Turkiyya ce za ta shirya taron COP31 na shekara mai zuwa a garin shakatawa na bakin teku na Antalya, bayan da Australia ta janye neman ta na ɗaukar nauyin wannan taro na shekara-shekara. Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce Turkiyya ta shirya karɓar baƙuncin taron Majalisar Ɗinkin D...

Turkiyya ce za ta shirya taron COP31 na shekara mai zuwa a garin shakatawa na bakin teku na Antalya, bayan da Australia ta janye neman ta na ɗaukar nauyin wannan taro na shekara-shekara. Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce Turkiyya ta shirya karɓar baƙuncin taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi na COP31 a watan Nuwamba mai zuwa, yayin da yake magana ga shugabanni a taron G20 da ake yi a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu. Turkiyya ce za ta shirya taron COP31 na shekara mai zuwa a garin shakatawa na bakin teku na Antalya, bayan da Australia ta janye neman ta na ɗaukar nauyin wannan taro na shekara-shekara. Yayin da yake jaddada manufofin makamashi na ƙasar, Erdogan a ranar Asabar ya ce manufar ita ce ninka ƙarfin samar da makamashin hasken rana da na iska sau huɗu zuwa shekarar 2035, kuma ya ce yanzu haka makamashin da ake samarwa maras gurɓata muhalli a Turkiyya ya haura kashi 60 cikin ɗari a wannan shekara. A kan batun Gaza kuwa, Erdogan ya yi nuni da cewa tsagaita wuta da aka cimma a watan da ya gabata tana da muhimmanci ga zaman lafiyar duniya. "A cewar bayanan Majalisar Dinkin Duniya, lalata wurare da Isra'ila ta yi ya mayar da hannun agogo baya a ci gaban Falaɗinu da shekaru 70 baya," in ji shi. Erdogan ya kara da cewa Turkiyya za ta ci gaba da dagewa wajen goyon bayan yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin da kuma bada gudummawa wajen sake gina Falasdinu. Johannesburg na karɓar baƙuncin wannan taron shugabanni na tsawon kwanaki biyu da nufin tattauna wasu daga cikin manyan ƙalubalen da duniya ke fuskanta.