Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano ta dakatar da nuna wasu fina-finai masu dogon zango 22

Hukumar, ta ce ta yi hakan ne a ƙoƙarinta na tabbatar dacewa ana bin dokar tace fina-finai sau da ƙafa tare da ƙara ɗora masana'antar Kannywood a kan saiti. Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano a Nijeriya ta sanar da dakatar da nuna wasu manyan f ina-finai masu dogon zango gar guda 22. A sanarwa...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:24
Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano ta dakatar da nuna wasu fina-finai masu dogon zango 22
Em resumo

Hukumar, ta ce ta yi hakan ne a ƙoƙarinta na tabbatar dacewa ana bin dokar tace fina-finai sau da ƙafa tare da ƙara ɗora masana'antar Kannywood a kan saiti. Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano a Nijeriya ta sanar da dakatar da nuna wasu manyan f ina-finai masu dogon zango gar guda 22. A sanarwa...

Hukumar, ta ce ta yi hakan ne a ƙoƙarinta na tabbatar dacewa ana bin dokar tace fina-finai sau da ƙafa tare da ƙara ɗora masana'antar Kannywood a kan saiti. Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano a Nijeriya ta sanar da dakatar da nuna wasu manyan f ina-finai masu dogon zango gar guda 22. A sanarwar da ta fitar ranar Litinin 19 ga watan Mayun 2025, mai ɗauke da sa hannun Abdullahi Sani Sulaiman Jami'in yada labarai na hukumar, ta ce ta yi hakan ne a ƙ oƙarinta na tabbatar da cewa ana bin dokar tace fina-finai sau da ƙ afa tare da ƙara ɗora masana'antar Kannywood a kan saiti . “ Hukumar tace fina-finai da ɗ ab'i ta ji har Kano ƙ ar ƙ ashin jagorancin Alh aji Abba El-mustapha ta dauki wani gagarun mataki domin tsaftace yadda ake sakin fina-finai barkatai ba tare da cika ƙa'idar da doka ta tanadar musu ba na kawo kowanne fim gabanta a tantance shi kafin ya isa ga idanun al'umma inda ta dakatar da wasu manyan f ina-finai har guda 22 daga saka su a kafafen Int a net ko gida je n talabijin,” in ji sanarwar. Sanarwar ta ƙara da cewa Abba El-mustapha ya bayyana wannan mataki biyo bayan tattaunawa da manyan jami'an h ukumar tare da dogon nazari domin kawo karshen ƙ orafe -ƙ orafen da hukumar take yawan karba don ƙ ara inganta a y yukan h ukumar tare da masana'antar Kannywood. Fina-finan da hukumar ta dakatar da nunawa sun haɗa da: 1. Dakin Amarya 2. Mashahuri 3. Gidan Sarauta 4. Wasiyya 5. Tawakkaltu 6. Mijina 7. Wani Zamani 8. Labarina 9. Mallaka 10. Kudin Ruwa 11. Boka Ko Malam 12. Wa yasan Gobe 13. Rana Dubu 14. Manyan Mata 15. Fatake 16. Gwarwashi 17. Jamilun Jiddan 18. Shahadar Nabila 19. Dadin Kowa 20. Tabarma 21. Kishiyata 22. Rigar Aro Sanarwar ta ce doka ce ta ba i wa hukumar damar tace duk wani fim tare da lura da a y yukan ‘yan masana'antar K annywood matsawar suna da r a jista da hukumar a ko ina suke . “ A saboda haka ana shawartar masu daukar nauyin wa ɗa nnan fina-finai da su tabbatar da sun bi wannan doka ta dakatarwa tare da tsayar da saka wa ɗa nnan fina-finai a gidajen talabijin ko int a net.” Haka kuma ana sanar da ma su shirya fina-finan cewa su mi ƙa fina-finansu ga hukumar domin tantance su tare da ba su shaidar inganci ta tacewa nan da sati daya mai zuwa wato daga L itinin , 18 ga watan M ayu z uwa 25 ga M ayun 2025 domin gujewa fushin doka. A karshe hukumar ta nemi hadin - kan dukkannin gidajen talabijin h ukumar da ke lura da kafafen yada labarai ta Nijeriya wato NBC kan su cigaba da taimaka mata domin samun nasarar abin da ta saka a gaba da cigaban j ihar Kano da masana'antar Kannywood.