الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Yansandan Jigawa Sun Kama Sabuwar Amarya Bisa Zargin Kashe Mijinta da Guba

Ana zargin ta saka maganin ɓera a abinci bayan aurensu Rundunar ‘Yansandan Nijeriya reshen Jihar Jigawa ta kama wata sabuwar amarya bisa zargin saka guba da ta yi sanadin mutuwar mijinta a ƙauyen Gauza da ke Ƙaramar Hukumar Jahun. Lamarin ya faru ne da yammacin ranar 23 ga Janairun 2026 bayan mar...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:07 ص
Yansandan Jigawa Sun Kama Sabuwar Amarya Bisa Zargin Kashe Mijinta da Guba
لمحة سريعة

Ana zargin ta saka maganin ɓera a abinci bayan aurensu Rundunar ‘Yansandan Nijeriya reshen Jihar Jigawa ta kama wata sabuwar amarya bisa zargin saka guba da ta yi sanadin mutuwar mijinta a ƙauyen Gauza da ke Ƙaramar Hukumar Jahun. Lamarin ya faru ne da yammacin ranar 23 ga Janairun 2026 bayan mar...

Ana zargin ta saka maganin ɓera a abinci bayan aurensu Rundunar ‘Yansandan Nijeriya reshen Jihar Jigawa ta kama wata sabuwar amarya bisa zargin saka guba da ta yi sanadin mutuwar mijinta a ƙauyen Gauza da ke Ƙaramar Hukumar Jahun. Lamarin ya faru ne da yammacin ranar 23 ga Janairun 2026 bayan marigayin ya ci abincin da matarsa ta shirya masa. (TRT Hausa) Bayan cin abincin, an ce marigayin ya kamu da mummunar rashin lafiya, inda aka gaggauta kai shi asibiti, sai dai daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa yayin da ake masa magani. Bayan faruwar lamarin, ‘yansandan sun ce sun garzaya wajen tare da kama wadda ake zargi. (TRT Hausa) A yayin bincike, wadda ake zargin ta amsa cewa ta saka maganin ɓera a cikin abincin mijin nata, tare da bayyana cewa ta aiki ɗanuwanta ne domin sayo maganin da ta yi amfani da shi wajen aikata laifin. (TRT Hausa) Ta kuma shaida wa jami’an bincike cewa an yi mata auren dole ne daga iyayenta, lamarin da ta ce ya kai ta ga aikata wannan ɗanyen aiki. (TRT Hausa) Kwamishinan ‘Yansandan Jihar Jigawa ya bayar da umarnin mika lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jiha (SCID) da ke Dutse domin zurfafa bincike, inda rundunar ta ce za a gurfanar da wadda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike. (TRT Hausa) Rundunar ‘Yansandan ta bukaci al’umma da su bi doka tare da neman hanyoyin shari’a wajen warware matsalolin aure da na iyali, tana mai gargadin jama’a da kada su ɗauki doka a hannunsu. (TRT Hausa)